An Kama Mutumin da Ake Zargin Yana Kai Wa ’Yan Bindiga Makamai a Plateau

An Kama Mutumin da Ake Zargin Yana Kai Wa ’Yan Bindiga Makamai a Plateau

  • Rahotanni sun bayyana cewa an kama wani mutum dauke da makamai a cikin wata jaka da ya ke yawo da ita a garin Jos, jihar Plateau
  • Wasu fusatattun matasa da suka fara damke mutumin, sun yi kokarin halaka shi bayan ganin makaman amma aka kira 'yan sanda
  • Mutumin da a ke fargabar mai safarar makamai ne ga 'yan bindiga ya bayyana cewa ya zo Jos ne daga Zamfara kuma ba shi kadai ba ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jos, jihar Filato - Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Plateau sun kama wani matashi mai matsakaicin shekaru da ake zargin yana kokarin kai wa ‘yan bindiga makamai a Jos.

Kara karanta wannan

Masarauta: 'Yan sanda sun goyi bayan Gwamnan Kano, an gargadi masu shirin rigima

An tattaro cewa wanda ake zargin ya isa garin Jos daga jihar Zamfara da yammacin Laraba, kuma an kama shi a lokacin da yake kokarin safarar makaman ga ‘yan bindiga.

'Yan sandan Plateau sun kama mai safarar makamai
'Yan sanda sun kama wani da ake zargi zai kai wa 'yan bindiga makamai a Jos. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Shugaban gidan shakatawa na NTA da ke Jos, Ibrahim Maikwudi, ya tabbatar wa jaridar Leadership faruwar lamarin a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maikwudi ya bayyana cewa wasu fusatattun mutane sun kusa halaka wanda ake zargin kafin jami’an tsaro suka karaso wurin tare da ceton shi.

"An kama mai safarar makamai" - Maikwudi

Shugaban gidan shakatawar ya ce wasu da ke zaune a yankin ne suka lura da take-taken wanda ake zargin, tare da hanzarin tara jama'a domin a kama shi.

"A lokacin da jama'a suka taru kan shi, an yi masa tambayoyi da ya kasa amsawa, nan ne aka kwace jakar da ke hannunsa inda aka same ta makare da makamai.

Kara karanta wannan

Mutane sama da 20 sun sutu a harin 'bam' da aka kai masallacin Kano

"A lokacin ne mutane suka yi kokarin yi masa dukan mutuwa amma muka yi gaggawar kiran 'yan sanda saboda muna tsoron kada mutanen su kashe shi."

- Ibrahim Maikwudi.

Wanda ake zargin ya yi magana

Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa cewa ba shi kadai ne ya shigo Jos ba, yana mai cewa akwai wasu da dama a harkallar safarar makaman, in ji rahoton Daily Post.

A halin da ake ciki, ba a iya samun jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar Filato, Alabo Alfred, kan lamarin ba saboda wayoyinsa na a kashe.

Gwamnati ta janye tuhuma kan Bodejo

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ofishin babban lauyan tarayya (AGF) ta janye karar da shigar kan shugaban Miyetti Allah, Bello Bodeji.

Gwamnati ta yi karar Bodeji ne a gaban babbar kotun tarayya kan tuhume-tuhume uku da suka shafi aikata ta'addanci bayan da ya kaddamar da kungiyar 'yan sa kai ta Fulani.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel