Sojoji sun Kara Samun Nasara, Sun Ragargaza 'Yan Ta'adda a Kaduna

Sojoji sun Kara Samun Nasara, Sun Ragargaza 'Yan Ta'adda a Kaduna

  • Rundunar sojojin Nigeriya ta bayyana cewa jami'anta sun kai harin kwantan bauna kan wasu 'yan ta'adda a jihar Kaduna har aka samu nasarar kashe 6 daga cikinsu
  • A sakon da rundunar ta wallafa a shafinta na x, ta bayyana cewa haka kuma cafke muhimman kaya irin su bindiga da kayan sufuri daga bata-garin da suka addabi al'umma
  • Sojojin sun yi wa yan ta'addar kwantan bauna a yankin Kidandan dake karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna, kuma sun fatattake su har ya zuwa kauyen Katoge

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna- Sojoji a jihar Kaduna sun yi nasarar ɗaiɗaiaita wasu 'yan ta'adda bayan harin kwantan-bauna da suka kai musu.

Kara karanta wannan

Rundunar sojojin Najeriya ta fatattaki 'yan ta'adda, an kamo miyagu a Abuja da Oyo

Sojoji
Sojoji sun kashe 'yan ta'adda 5 a Kaduna Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

An yiwa 'yan ta'addar raga-raga a yankin Kidandan dake karamar hukumar Giwa, wanda ya tilastawa bata-garin guduwa da suka ji akan wuta.An yiwa 'yan ta'addar raga-raga a yankin Kidandan dake karamar hukumar Giwa, wanda ya tilastawa bata-garin guduwa da suka ji akan wuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A sanarwar da rundunar ta wallafa a shafinta na x, ta ce 'yan ta'addar sun gudu saboda da ruwan harsashi daga sojojin, inda suka bar bindiga kirar pistol.

Sojoji sun kori yan ta'adda a Basurfe

Rahotanni sun bayyana yadda sojojin Najeriya suka kori wasu 'yan ta'adda kauyukan Basurfe da Yuna a Kaduna inda suka koro wasu 'yan ta'adda.

Leadership News ta wallafa cewa 'yan ta'addar sun tsere inda suka bar babur guda daya, suka kuma tsallaka kogi domin neman tsira.

Rundunar sojojin kasar nan ta ce jami'anta ba su tsaya wata-wata na sai suka bi sawunsu zuwa kauyen Katoge inda aka yi arangama har aka kashe miyagu biyar

Kara karanta wannan

Layyah: Ana shirin babbar sallah, gwamnati na yiwa jama'a gargadin guba a jikin dabbobi

'Yan bindiga sun kaiwa 'yan majalisa hari

A baya mun ruwaito muku cewa wasu 'yan majalisa guda biyar sun tsallake rijiya da baya bayan 'yan bindiga sun kai musu hari a titin Makurdi zuwa Gboko a jihar Benue.

Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun budewa tawagar 'yan majalisar jihar wuta da misalin karfe 10.00 na dare a kauyen Tyomu mai nisan kilomita 16 zuwa babban birnin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel