Zargin Ta’addanci: Kotu Ta Sallami Shugaban Miyetti Allah Bayan Wata 4 a Tsare

Zargin Ta’addanci: Kotu Ta Sallami Shugaban Miyetti Allah Bayan Wata 4 a Tsare

  • Mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya ya sallami shugaban Miyetti Allah Kautal, Bello Bodejo daga tuhumar ta’addanci
  • Babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) ne ya gabatar da bukatar janye karar da gwamnatin ta shiga kan Bodejo saboda a yi adalci
  • An kama Bodejo a watan Janairun 2024 a ofishin Miyetti Allah da ke Karu, jihar Nasarawa kan kaddamar da kungiyar ‘yan banga

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wata babbar kotun tarayya ta sallami shugaban Miyetti Allah Kautal Kore, Alhaji Bello Bodejo daga tuhumar da gwamnatin tarayya ke yi masa na ta’addanci.

Mai shari’a Inyang Ekwo, a wani dan takaitaccen hukunci, ya sallami Bodejo bayan da lauyar gwamnati, Aderonke Imana ta gabatar da bukatar a janye tuhumar da ake masa.

Kara karanta wannan

Wa zai zama Sarkin Kano? Abin da kotuna 2 suka ce game da makomar Sanusi II da Aminu

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar gwamnati da shugaban Miyetti Allah
Kotu ta sallami shugaban Miyetti Allah da gwamnati ke zargin ya aikata laifin ta'addanci. Hoto: Miyetti Allah Kautal Hore, Officialasiwajubat
Asali: Facebook

A zaman shari'ar da aka ci gaba da yi a ranar Laraba, Imana ta sanar da kotun cewa tana da bukatar da za ta gabatar ta baki, in ji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Miyetti Allah: Gwamnati ta janye karar Bodejo

Lauyar ta ce bukatar ta kasance a karkashin sashe na 108 na dokar kula da shari’a ta laifuffuka (ACJA), da aka yi a 2015.

Ta ce bukatar tana da nasaba da karfin ikon babban lauyan tarayya AGF da ya samu a karkashin sashe na 174 na kundin tsarin mulkin 1999 (wadda aka sabunta).

Jaridar The Cable ta ruwaito Imana ta kara da cewa babban lauyan gwamnatin tarayya ya umarce ta da ta janye tuhumar da ake yiwa wanda ake kara a bisa doron adalci na shari'a.

Kotu ta sallami shugaban Miyetti Allah

Tawagar lauyoyin Bodejo ba su yi adawa da wannan bukatar ta Imana ba.

Kara karanta wannan

An gina tasha mai otel, gareji da ofisoshi da za ta rika daukar motoci 5000 a rana

A cikin hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Inyang Ekwo ya ce:

“Bayan duba wannan bukatar, kotu ta ba da umarni a saki wanda ake tuhuma. Wannan shi ne umarnin wannan kotun."

Yadda aka kama Bodeji a Nasarawa

Tun da fari, mun ruwaito jami'an tsaro sun kama Bodejo a ranar 23 ga watan Janairu a ofishin Miyetti Allah da ke karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa.

An kama Bodejo ne biyo bayan kaddamar da kungiyar ‘yan banga ta Fulani a jihar, abin da gwamnati ta kira barazana ga tsaron kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel