'Yan Sanda Sun Cafke Masu ba 'Yan Ta'adda Bayanan Sirri, Sun Kashe Miyagu a Kaduna

'Yan Sanda Sun Cafke Masu ba 'Yan Ta'adda Bayanan Sirri, Sun Kashe Miyagu a Kaduna

  • Hadakar jami'an tsaro a jihar Kaduna sun fatattaki yan ta'adda a yankin Nasarawar Azzara-Dogon-Fili a yankin Katari da ke karamar hukumar Kachia
  • Wani mazaunin garin ya bayyana cewa 'yan bindigar sun sace yaran wani likita wanda hakan ya sa gamayyar jami'an bibiyar sawun 'yan bindigar
  • Daga bisani jami'an sun samu nasarar kashe 'yan ta'adda, inda a rana guda wasu jami'an tsaro suka damke masu bawa 'yan ta'adda bayanan sirri a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna- Wasu yan ta’adda a jihar Kaduna sun gamu da gamonsu bayan hadakar jami’an tsaro suka ragargaza maboyarsu dake yankin Nasarawar Azzara-Dogon-Fili a yankin Katari dake karamar hukumar Kachia.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kaduna ta daura damarar yakar yan ta'adda, ta ba jami'an tsaro tallafi

Wani mazaunin yankin, Saleh Kabiru ya bayyana cewa jami’an tsaron da suka yi aiki tare da ‘yan bijilanti sun farmaki maboyar miyagun a dajin da suke.

Yan sanda
Jami'an tsaro sun yi galaba a kan miyagu a Kaduna Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa dama jami’an tsaron na ta bin sawun bata garin da suka sace wasu yaran wani likita guda uku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan ta'adda sun fara bude wuta,’ Kabiru

Wani mazaunin Nasarawar Azzara-Dogon-Fili a yankin Katari dake karamar hukumar Kachia a Kaduna, Saleh Kabiru ya bayyana yadda jami’an tsaro suka so yiwa jami’an tsaro kofar rago.

Ya shaidawa manema labarai ‘yan bindigar sun hau bishiyoyi a lokacin da suka fuskanci cewa jami’an tsaron suna tunkaro su.

Saleh Kabiru ya bayyana cewa ‘yan ta’addar sun raba kawunansu gida uku sannan suka sauyawa yaran da suka sace matsuguni, kamar yadda City and Crimes ta wallafa.

Masu ba 'yan ta'adda sirrin mutane

Kara karanta wannan

An dauki mataki kan 'dan sandan da aka nadi bidiyonsa yana karbar 'na goro' a Imo

Haka kuma jami'an sun damke wasu mutum biyu da ake zargi da bawa yan ta’adda bayanan sirri a yankin Katari, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Hassan Mansur ya tabbatar.

A yau ana fama da masu matsalar masu taimakawa 'yan bindiga da bayanan sirri.

An kashe mutum biyu a Kogi

A baya mun kawo muku labarin cewa mutane biyu sun mutun yayin wata arangama tsakanin jami'an tsaro da masu garkuwa da mutane a jihar Kogi.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi arangamar ne a a dajin Ankumi dake jihar Kogi da wadanda ake zargi da sace kayan mutane, sannan an kwato kayayyaki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel