Gwamnatin Najeriya
Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya ce wutar lantarki za ta wadata a Nijeriya nan da shekara uku, amma gwamnati za ta janye tallafin wutar gaba ɗaya zuwa lokacin.
Ministan cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ola ya fitar da sanarwa a madadin gwamnatin tarayya cewa ranar Talata da Laraba za su zama ranakun hutu domin bikin Sallah.
Wani dan Najeriya ya bayyana yadda ya siya kati mai tsada bayan da gwamnati ta kara farashin wutar lantarki a makon da ya gabata kan wasu dalilai.
Fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwar cewa Bola Ahmed Tinubu zai gudanar da bikin karamar Sallah a Legas. An ruwaito cewa zai bar Abuja ranar Lahadi.
Akalla dai anguwanni 481 ne ke karkashin sahun farko a ba da wutar lantarki a Nijeriya. Wadannan anguwanni na samun wutar ta awa 20 a kowacce rana.
An ji abin da ya jawo NERC ta laftawa kamfanin AEDC tarar N200m. AEDC ya rika saida wutar lantarki ga duka abokan hulda da cinikinsa a kan sabon farashin Band A.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana daukar matakai na janye tallafin wutar lantarki, ciki har da karin kudin wutar da kuma ba da 'yan kasuwa damar zubar jari.
Asusun bayar da lamuni ga daliban Najeriya, a ranar Laraba ya ce za a fara kaddamar da shirin ne da daliban manyan makarantu na gwamnati, ban da na kudi.
Yayin da hukumar NERC ta sanar da karin kudin wutar lantarki a Najeriya, an yi ta cece-kuce kan matsalar wutar da rashin ingancinta musamman a watan Ramadan.
Gwamnatin Najeriya
Samu kari