Kasar Qatar Ta Turo Sakonni 3 ga Shugaba Tinubu kan Hatsarin Jirgin Sojojin Najeriya

Kasar Qatar Ta Turo Sakonni 3 ga Shugaba Tinubu kan Hatsarin Jirgin Sojojin Najeriya

  • Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al-Thani, ya aika saƙon ta’aziyya ga Shugaba Bola Tinubu kan mutuwar mutane hatsarin jirgin sojin saman Najeriya
  • Mataimakin Sarkin Qatar da Firaministan ƙasar, wanda kuma shi ne ministan harkokin waje, sun aika da nasu saƙonnin ta’aziyyar
  • Tinubu ya ayyana kwanaki uku na zaman makoki na ƙasa tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan musabbabin hatsarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Qatar - Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al-Thani, ya turo saƙon ta’aziyya ga Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, kan mutuwar fasinjoji da ma’aikatan jirgi sakamakon hatsarin jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya.

Mataimakin Sarkin Qatar, Sheikh Abdullah bin Hamad Al-Thani, da Firaministan ƙasar kuma Ministan Harkokin Waje, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al-Thani, sun aika da saƙonnin ta’aziyya daban-daban ga shugaban Najeriya.

Kara karanta wannan

2027 da magana: Dubban mutane sun yi gagarumin gangami a Arewa saboda Tinubu

Sarkin Qatar.
Sarkin kasar Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Shugabannin Qatar 3 sun yi ta'aziyya

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugabannin Qatar uku sun aika wa Tinubu saƙonnin ta’aziyya ta hanyar wasiƙu dangane da waɗanda suka rasu a hatsarin.

Hatsarin ya faru ne a ranar 5 ga Oktoba, lokacin da wani jirgin ATR-42 na Rundunar Sojin Saman Najeriya ya faɗi a wani yanki mai dausayi kusa da sansanin sojojin ruwa da ke Igbokoda, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Ilaje a jihar Ondo.

A cewar Rundunar Sojin Saman Najeriya, jirgin yana gudanar da wani aikin yau da kullum ne daga birnin Benin da ke jihar Edo zuwa Legas lokacin da hatsarin ya faru.

Matakan da aka dauka bayan hatsarin

Bayan hatsarin, rundunar ta fara gudanar da aikin nema da ceto. Daga baya ta bayyana cewa mutane 25 ne ke cikin jirgin, ciki har da ma’aikatan jirgi biyar da fasinjoji 20, tare da tabbatar da cewa babu wanda ya tsira.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwa kan duban jinjirin watan Musulunci a Najeriya

Bayan wannan mummunan lamari, Tinubu ya ayyana kwanaki uku na zaman makoki na ƙasa, tare da bayar da umarnin saukar da tutocin ƙasa zuwa rabi a faɗin Najeriya.

Shugaban ƙasar ya kuma bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin hatsarin.

Tun daga lokacin, Rundunar Sojin Saman Najeriya ta fara ƙoƙarin gano na’urorin adana bayanan jirgin da na muryoyin matukan jirgi a wurin da hatsarin ya faru.

Dangantakar Qatar da Najeriya

Saƙon ta’aziyyar Qatar ya zo ne a daidai lokacin da ƙasashen biyu ke ƙoƙarin ƙarfafa dangantakarsu ta diflomasiyya da tattalin arziki, tare da faɗaɗa haɗin gwiwa da sauran ƙasashen Afirka.

Shugaba Bola Tinubu.
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a fadar White House Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

A watan Mayun 2025, Shugaba Tinubu ya yi maraba da sababbin shirye-shiryen zuba jari daga Qatar, musamman a fannin noma da samar da isasshen abinci.

Ya kuma sake jaddada aniyar Najeriya ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu yayin da Gwamnatin Qatar ta kuma nuna sha’awarta ta faɗaɗa haɗin gwiwa da Najeriya a wasu muhimman fannoni.

Turkiyya ta taya Najeriya alhini

Kun ji cewa Gwamnatin Turkiyya ta miƙa saƙon ta’aziyya ga Najeriya kan hatsarin jirgin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) da ya yi sanadin mutuwar mutane 25.

Turkiyya ta ce ta yi matuƙar baƙin ciki kan asarar rayukan da hatsarin jirgin sojin ya haddasa a Jihar Ondo ranar 5 ga Oktoba, 2026, lamarin ya jefa iyalai da dama cikin jimami.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262