Gwamnatin Tarayya Ta Bada Sharadin Rage Kudin Wutar Lantarki

Gwamnatin Tarayya Ta Bada Sharadin Rage Kudin Wutar Lantarki

  • Adebayo Adelabu, ministan wutar lantarki, ya bayyana sharadin da zai sa a rage kudin wutar lantarki yayin wata hira da 'yan jarida da ya yi ranar Alhamis
  • Duk da haka, ministan ya tabbatar da cewa karin kudin zai amfani al'ummar kasar saboda sun nemi shawarwari daga masana kafin yanke hukuncin
  • Bayanan nasa sun biyo bayan suka da gwamnatin ke cigaba da sha ne sakamakon karin kudin wuta wa 'yan rukunin Band A

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Adebayo Adelabu, ministan wutar lantarki, ya bayyana sharadin rage kudin wutar lantarki yayin wata hira da yayi da 'yan jarida.

Bayanan na shi sun biyo bayan suka da 'yan Najeriya suka yawaita bayan kara kudin wutar ga 'yan rukunin Band A da gwamnatin tayi.

Kara karanta wannan

Bikin Sallah: 'Yan sanda a Kano sun kama mutum 54 masu yunkurin hargitsa hawan sallah

Tinubu lantarki
Gwamnatin tace dole sai farashin dala ya sauka kafin a rage kudin wutar lantarki. Hoto: Bola Ahmed Tinubu Asali: Facebook
Asali: Facebook

Sharadin rage kudin wutar lantarki

Ministan ya bayyana sharadin ne yayin da yake magana a wata hira da aka yi da shi tare da 'yan jarida ranar Alhamis, cewar jaridar Daily Trust

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa N225 a kowanne kilowat da masu amfani da wutar lantarki ke biya a rukunin Band A zai ragu idan farashin dala ya dawo kasa da N1,000.

Meyasa aka kara kudin lantarki?

A cikin hirar ta shi, ministan ya bayyana babban dalilin da yasa aka samun karin kudin wutar wa 'yan rukunin Band A.

A cewarsa, tashin dala ya yi tasiri sosai a kan tashin kudin wutar. Saboda haka ne ma bazai yiwu a rage kudin ba har sai dala ta sauko kasa da ₦1,000.

Ya kuma kara da cewa gwamnatin ta tuntubi masana da masu ruwa da tsaki a harkar tun kafin karin kuɗin.

Kara karanta wannan

Tsohon dan takarar shugaban kasar Nijeriya, Ogbonnaya Onu ya rasu

Saboda haka ne yayi kira ga 'yan Najeriya da su rungumi sabon tsarin domin da niyyar gyara aka kawo sa. Ga abin da yake cewa:

“Mun yi shawarwari da yawa kafin mu isa kan karin kudin. Akwai masu ruwa da tsaki da dama a fannin wutar lantarki da suka hada da masu aikin samar da wutar lantarki da kamfanonin samar da wutar lantarki da kamfanonin sadarwa da kwastomomi da ma’aikata”.

Gwamnati za ta kara kudin wuta

A wani rahoton kuma, kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta ce akwai shiri na kara kudin wutar lantarki bayan da ta sanar da karin kudin ga kwastomomi 'yan layin BAND A.

Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ne ya bayyana hakan yana cewa gwamnati ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin wutar lantarki ba saboda yawan kudin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel