Yan Najeriya Sun ƙi Amincewa da Biyan Harajin ₦3000 Domin Hawa Babban Titin Legas-Calabar

Yan Najeriya Sun ƙi Amincewa da Biyan Harajin ₦3000 Domin Hawa Babban Titin Legas-Calabar

  • Wasu ƴan Najeriya sun nuna rashin amincewarsu kan Naira ₦3000 da gwamnatin tarayya ta ce za ta karba a matsayin haraji
  • Ministan ayyuka, Dave Umahi ya bayyana yadda gwamnatin ke kokarin ganin motocin da za su bi hanyar na biyan ₦1500, manyan motoci kuma ₦5000
  • Kungiyoyi na ganin ₦300 ya kamata ƴan Najeriya su biya a matsayin haraji duba da ƙangin da ake ciki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Adana, Calabar - Ƴan ƙasar nan sun fusata bayan an jiyo gwamnatin tarayya na cewa masu bin titin Legas-Kalaba da ake ginawa za su rika biyan ₦3000 a matsayin haraji kullum idan titin ya kammala. Ministan ayyuka, Dave Umahi ne ya fadi kuɗin da ake sa ran masu sufurin za su biya kamar yadda ya bayyana a rahoton Vanguard News.

Kara karanta wannan

SSANU da NASU: Gwamnatin tarayya za ta biya rabin albashin ma'aikatan da ta rike

“Na sanya ₦3,000 a matsayin madaidaicin kuɗin da za a biya. ₦3,000 saboda motocin hawa za su biya kamar ₦1,500, manyan motoci kuma za su biya kamar ₦5,000."

- David Umahi

Babban Titin Legas-Kalaba: Ƴan Najeriya Sun ƙi Amincewa da Biyan Harajin ₦3000
Idan titin ya kammala, masu bin hanyar ka iya biyan har N3000 a matsayinn haraji Hoto: Governor David Nweze Umahi
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan Najeriya sun yi fatali da harajin

Daga cikin waɗanda suka yi fatali da kuɗin da gwamnatin ta ƙayyade za a biya akwai gamayyar jam'iyyun siyasa (CUPP). Sakataren gamayyar, Cif Peter Ameh, ya shaidawa Vanguard cewa, duk harajin da ya wuce ₦300 zai ƙara jefa talakawan ƙasar nan cikin halin ni-ƴa-su.

Bayan CUPP, wasu daga kungiyoyin da ɗaiɗaikun mutanen da suka nuna rashin amincewa da harajin akwai tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da kungiya kwadago ta NLC, da jam'iyyar LP, da kungiyar dattawan Neja Delta PANDEF da wasu ƙungiyoyin sufuri.

Zargin rufa-rufa a aikin babban titi

A makon da ya gabata, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin tarayya da rashin gaskiya wajen bayar da kwangilar babban titin Legas-Kalaba. Ya ce gwamnatin ta tsallake matakan da doka ta shimfiɗa wajen bayar da kwangilar irin waɗannan ayyukan, da ma wasu zarge-zargen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel