“Mun Shiga Uku”: Dan Najeriya Ya Sha Tsada Bayan Siya Katin Wutar Lantarki Na N400,000

“Mun Shiga Uku”: Dan Najeriya Ya Sha Tsada Bayan Siya Katin Wutar Lantarki Na N400,000

  • Wani matashi dan Najeriya ya kai ziyara ofishin PHCN don sake siyan katin wutar lantarki, ya ba da labarin abin da ya gani
  • A cewar fusataccen mutumin, ya samu ragin adadin 1,300 na katin wuta wanda darajarsa ya kai akalla N140,000
  • Jama'a a kafar sada zumunta sun yi ca a sashen sharhi yayin da ya yada labarin abin da ya faru dashi a shafinsa na Twitter

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Wani dan Najeriya mai suna Ichbin Eugene ya bayyana kokensa mai zafi a manhajar Twitter kan yadda ya sayi katin wutar lantarki mai darajar N400,000.

Ya siya katin ne kwanaki kadan bayan da gwamnatin Najeriya ta sanar da karin 300% ga kwastominin wuta da ke kan tsarin 'Band A'.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta ci kamfanin AEDC tarar N200m saboda zaluntar mutane wajen shan lantarki

Yadda dan Najeriya ya sha tsada wajen siyan katin lantarki
Dan Najeriya ya sha tsada a siyan katin wutar lantarki | Hoto: Ichbin Eugene/ X. (Hoton da ke jiki bai da alaka da mutumin da ake magana a kansa a labarin, an saka ne don surantawa)
Asali: Twitter

An rage min yawan kati akalla 1,300

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake bayyana kokensa a Twitter, Eugene ya kwatanta yadda ya sayi katin a baya kafin a samu karin da gwamnati ta yi.

Ya nunawa dubiya rasitin siyan katin, wanda aka nuna ya sayi dango adadin unit 1967.27 a kan kudi N400,000.

A cewarsa, wannan babban kalubale ne idan aka kwatanta da yadda a baya ya sayi wutar cikin kwanciyar hankali.

A cewar Eugene, hakan na nufin an zaftare masa unit na wuta akalla 1,311.51 wanda idan aka lissafa kudinsa ya kai N140,000.

Jama'a sun yi martani kan karin kudin wutar lantarki

Jama'ar kafar sada zumunta sun yi martani mai daukar hankali a sashen sharhin rubutun Eugene, inda suka bayyana halin da suke ciki. Ga kadan daga ciki:

Supakey yace:

"Kuma kowa na gunaguni a daki. Daga karshe dai kowa zai koma Band A. Dabarar itace, a sauran yankuna: za ku sami wutar awa 18 a cikin kamar sati 2, suna kara farashi sannan su koma ga yadda yake a baya na akalla awa 3 a rana ko kuma su dauke wutar kwata-kwata."

Kara karanta wannan

NERC ta tsokano ‘yan kwadago, ana yi wa Tinubu barazana saboda kudin lantarki

Empress Chi yace:

"Lallai jama'a da yawa a kasar nan na da arziki, N400k a siyan katin wuta."

Mucawon yace:

"Dukkan ma'aikatun gwamnati ciki har da fadar shugaban kasa ana binsu bashin kudin wuta amma suna samun wuta. Talaka ne ake takurawa ya biya a madadinsu."

Amakzee tace:

"Daga karshe kuma sai ka siya mai don taimakawa wannan. Kamar dai 400k a wata zai koma maka 600k a wata. Muna cikin matsanancin hali! Za a yi ta cewa dala ta sauka amma kaya na tashi. Da wannan tsadar wuta, ta yaya za a samu ribar kasuwanci?"

Inda wutar lantarki za ta yi tsada

A wani labarin, hukumar da ke sa ido kan wutar lantarki ta Najeriya (NERC), ta amince da karin kudin wuta ga unguwanni 481 da ke a sahun farko (Band A).

Takardun da aka samu daga hukumar sun nuna cewa kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja, AEDC, yana da unguwanni 107 a karkashinsa.

Hakazalika, an bayyana na sauran kamfanoni da kuma adadin da ake sa ran za su fara biya nan ba da jimawa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel