Karin Kudin Wuta: Gwamnati Ta Dauki Mataki 1 Na Wadatar da Wutar Lantarki a Nijeriya

Karin Kudin Wuta: Gwamnati Ta Dauki Mataki 1 Na Wadatar da Wutar Lantarki a Nijeriya

  • Gwamnatin tarayya, ta ce ta za ta janye tallafin wutar lantarki domin wadatar da wutar a Nijeriya nan da shekara uku masu zuwa
  • Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya bayyana hakan a Abuja, inda ya ce 'yan Nijeriya su shirya biyan kudin wuta da tsada
  • Janare Bature, daga jihar Katsina, wanda ya zanta da Legit Hausa, ya ce 'yan Nijeriya za su samu ayyukan yi idan wuta ta wadata a kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta shirya bayar da wutar lantarki awa 20 a fadin Nijeriya nan da shekara uku, kamar yadda ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya ayyana.

Gwamnati ta yi magana kan wadatar da wutar lantarki a Nijeriya
Gwamnati ta ce nan da shekara 3 za ta mayar da gaba 'yan Nigeria kan tsarin 'Band A'. Hoto: @BayoAdelabu
Asali: Facebook

"Zamu cire tallafin wutar lantarki" - Adelabu

Kara karanta wannan

Eid-el-Fitr: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranaku 2 na hutun Sallah

Gwamnatin za ta cimma wannan kudirin ne ta hanyar mayar da duka 'yan Nijeriya kan tsarin Band A, wadanda ke samun wuta awa 20 a rana, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi a wani taron bita na mako-mako a Abuja, ministan ya ce gwamnati ta yi karin kudin lantarki a wani yunkuri na daina biyan tallafin wutar gaba daya.

A cewar Adelabu, gwamnatin tarayya na kashe akalla N2.9trn wajen biyan tallafin lantarki, inda ya ce har yanzu gwamnati za ta biya kaso 85% na kudin wutar da ake sha a kasar.

"Wuta za ta wadata a shekara 3" - Adelabu

Ministan ya ce:

"Mun yanke shawarar karin kudin wutar lantarki domin rage kudaden da muke kashewa wajen biyan tallafi. Da wannan ne wutar za ta iya wadata, mu ce nan da shekara uku.

Kara karanta wannan

Mafita mafi sauki: Reno Omokri ya ba 'yan Najeriya shawarin yadda za su shawo kan karyewar Naira

"Gwamnati ta duba halin da ake ciki ne ya sa ba ta janye tallafin kai tsaye ba, amma a halin yanzu ba za mu iya ci gaba da biyan tallafi ba."

Adelabu ya kuma bayyana cewa janye tallafin wutar zai ba manyan 'yan kasuwa damar zuba hannun jari, wanda zai sa wutar ta wadata duk da cewa za ta yi tsada a nan gaba.

"Talaka zai samu tallafin wuta" - Minista

Jaridar This Day ta rahoto ministan ya ce har zuwa lokacin da gwamnati za ta janye daga biyan tallafin wutar gaba daya, wadanda ba sa karkashin Band A, za su sami tallafin kaso 70% .

Sai dai ya ce a yanzu mutane miliyan 1.5 ne kawai karin kudin ya shafa, amma sauran 'yan Nijeriya su shirya biyan kudin wutar da tsada nan gaba.

Ya jaddada cewa, ta hanyar janye tallafin wutar ne kawai wutar za ta wadata a kasar, ta yadda kowa zai iya komawa kan sahun Band A, da ke samun wuta awa 20 a rana.

Kara karanta wannan

Karin kudin wuta: Kano da sauran jihohi 12 da suka shirya inganta wuta ga al'ummarsu

Talaka zai amfana idan wuta ta wadata? A zantawar da Legit Hausa ta yi da Janare Bature daga jihar Katsina, ya ce matsin tattalin da ake ciki ne kawai zai sa talaka ya ga rashin amfanin karin kudin wutar lantarki. Bature ya ce talaka zai iya shiga mawuyacin hali da farko amma tabbas akwai fa'ida a karin kudin, tunda wutar za ta wadata ne. Ya ce idan har wutar lantarki ta wadata ga talaka, zai zamana cewa sana'o'i sun yawaita, hanyar samun arziki ta karu. A cewar shi rashin wadatacciyar wuta ya jawo kananan kamfanoni da sana'o'i sun durkushe , wanda kuma ya tilasta mutane da yawa rasa ayyukan yi. Bature ya yi kira ga gwamnati da ta kara wa'adin da ta dauka na janye tallafin wutar lantarki gaba daya, ya ce har yanzu talaka bai farfaɗo daga matsin tattali ba.

Anguwanni 481 da ke karkashin 'Band A'

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa anguwanni 481 ne ke karkashin sahun 'Band A' wadanda ke samun wutar lantarki ta awanni 20 a rana.

Wadannan anguwannin su ne wadanda gwamnati ta kara wa kudin wutar lantarki a baya-bayan nan daga N66/KwH zuwa N225KwH, lamarin da ya jawo cece-kuce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel