Bincike Ya Nuna Farashin Cinikayya a Najeriya ya Ninka na Amurka Sau 5

Bincike Ya Nuna Farashin Cinikayya a Najeriya ya Ninka na Amurka Sau 5

  • Bankin Duniya ya ce farashin cinikayya a Najeriya ya fi na Amurka sau biyar saboda dalilai da dama ciki har da rashin kyawun hanyoyi a kasar
  • An gano karuwar farashin cinikayya a kasashen nahiyar Afirka 14 cikin 40 da ake da bayanan yadda farashin kayayyakin abinci a kasashen ke tafiya
  • Bankin na ganin baya ga rashin kyawun hanyoyi a Najeriya,rashin rige-rigen 'yan kasuwa wajen sanya hannun jari a bangaren sufuri ya taimaka wajen ninkuwar farashin cinikayyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Najeriya- Wani Rahoton Bankin Duniya ya nuna farashin cinikayya a Najeriya ya ninka na kasar Amurka sau hudu zuwa biyar.

Kara karanta wannan

Yayin da ya fara fitar da mai, Dangote ya samo mafita kan tsadar kayayyaki a Najeriya

A rahoton Bankin, wannan na da alaƙa da rashin tsaro, tsadar sufuri da rashin kyawun hanyoyin ƙasar, kamar yadda The Guardian ta wallafa.

Farashin cinikayya a Najeriya ya ninka na kasar Amurka sau 5
Bankin Duniya na ganin rashin kyawun hanyoyin kasar nan ya taimaka wajen ninkuwar farashin Hoto: Getty images
Asali: Getty Images

Rahoton bankin duniya a kan Najeriya

Rahoton ya kara da cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

" Ana samun kalubale wajen shiga kasuwar samfurin kayayyaki,wanda hakan ke hana kamfanoni da manoma ƙara samar da kayayyaki. Rashin haɗe kasuwanni da rarrabuwarsu ya bai wa kamfanoni damar kutsawa cikin kasuwanni su yi abinda suka ga dama."

A cewar bankin, hakan yana taimakawa wajen rashin daidaituwar samu tsakanin al'umma.

Farashi na hauhawa a Afirka

A cewar rahoton Bankin Duniya, tun a watan Fabrairun 2024 aka samu hauhawar farashi a ƙasashe 14 cikin 40 da ake da bayanai kan farashin kayan abincin da ake sayarwa a kasashen.

An gano wadannan ƙasashe, ciki har da Najeriya, Malawi, Ethiopia, Sierra Leone da Zimbabawe sun samu hauhawar farashin sosai.

Kara karanta wannan

Tsohon dan takarar shugaban kasar Nijeriya, Ogbonnaya Onu ya rasu

Rahoton na ganin a Najeriya, tsadar cinikayyar ya biyo bayan rashin hanyoyi masu kyau da rashin masu rige-rigen sanya hannun jari a ɓangaren sufuri.

A ganin bankin rashin rige-rigen cinikayya zai daƙile ƙirƙirar sabbin dabarun kasuwanci a ƙasar.

Ana samun talauci saboda hauhawar farashi

A baya, Bankin Duniya ya yi gargadin samun karuwar talauci a Najeriya saboda hauhawar farashi.

Bankin ya ce mutum miliyan 2.8 ne za su fada kangin talauci a Najeriya daga 2023 zuwa 2024.

Asali: Legit.ng

Online view pixel