Gwamnatin Jihar Kogi Ta Koka Kan Rashin Samun Wadataccen Tallafin Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Jihar Kogi Ta Koka Kan Rashin Samun Wadataccen Tallafin Gwamnatin Tarayya

  • Gwamnatin Kogi ta bayyana dalilai da suka jawo har yanzu bata samu damar raba abincin tallafi ga al'umma ba
  • Ta zargi gwamnatin tarayya da direbobin da aka bai wa jigilar kayan da sakaci wajen rashin zuwan tallafin akan lokaci
  • Gwamnan jihar ya yabawa al'ummar Kogi akan hakuri da juriya da suka yi kan rashin tada hankali domin rashin samun tallafin akan lokaci

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum

Gwamnatin jihar Kogi ta ba da uzuri akan rashin raba tallafin abinci da gwamnatin tarayya ta turo jihar inda ta daura laifin akan rashin isowar dukkanin kayan tallafin akan lokaci.

Tallafin abinci da jihar Kogita samu
Abincin tallafi da jihar Kogi ta samu daga FG
Asali: Facebook

Sakataren hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Mouktar Atimah ne ya bayyana haka ranar Lahadi, inda ya bayyana cewa jihar ta samu kusan kashi 95% na tallafin gwamnatin tarayya a karkashin hukumar ba da agajin gaggawa.

Kara karanta wannan

Karin kudin wuta: Kano da sauran jihohi 12 da suka shirya inganta wuta ga al'ummarsu

Sakataren ya daura laifin rashin isowar sauran kayan tallafin akan direbobin da gwamnatin tarayya ta daurawa nauyin su jihar Kogi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabi sakataren SEMA

Jaridar Tribune ta ruwaito sakataren yana cewa:

"Tallafin abincin da aka warewa jihar Kogi har yanzu bai iso gaba daya ba saboda jinkirin da aka samu daga banagaren masu dauko kayan."

Ya kara da cewa gwamnan jihar, Alhaji Usman Ododo da hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar, a karkashin jagorancinsa.

Hakazalika, ya yabawa al'ummar jihar kan hakuri, juriya da ci gaba da goyon bayan gwamnatinsa duk da rashin samun wadataccen tallafin akan lokaci, rahoton Punch.

Gwamnatin tarayya za ta raba kayan abinci kyauta

A wani labarin kuma, gwamnatin tarayya ta yi alkawarin raba kayan abinci ga daukacin jihohin kasar kyauta domin rage radadin matsin tattalin arzikin da kasar ke fama dashi.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta ce za ta kuma kara kudin wutar lantarki, ta fadi dalili

Ministan noma da kayan abinci, Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wani sako da ya bayyana a Manhajar X, kuma ya bayyana cewa tallafin zai saukaka tsananin da 'yan Najeriya ke fama da shi.

Ministan ya tabbatar da za a fara rabon kayan abincin cikin makon nan kuma za a fara raba tan 42,000 na hatsi a jihohi 36 kamar yadda shugaban kasa ya bada umarni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel