Fadan Cikin Gida: Malamin Musulunci Sun Fara Adawa Shugaban Hukumar Alhazai

Fadan Cikin Gida: Malamin Musulunci Sun Fara Adawa Shugaban Hukumar Alhazai

  • Malaman Musulunci a Osun sun yi watsi da yunkurin tsawaita wa shugaban hukumar jin daɗin alhazai wa’adin shugabancinsa
  • Majalisar malaman ta ce Isola ya shafe shekaru takwas yana shugabancin hukumar, kuma tsawaita wa’adinsa zuwa 2030
  • Malaman sun bukaci Gwamna Ademola Adeleke ya bai wa yankunan da ba su taɓa samar da shugaban hukumar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - Malaman Musulunci a jihar Osun sun tura sako ga gwamna kan shugaban hukumar alhazai.

Malaman sun yi Allah-wadai da zargin shirin tsawaita wa’adin shugaban hukumar jin daɗin alhazan jihar, Dakta Moruf Isola, bayan shekarar 2026.

Malamai sun taso shugaban hukumar alhazai a Osun
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun. Hoto: Governor Ademola Adeleke.
Source: Twitter

A cikin wasiƙar da suka aika wa Gwamna Ademola Adeleke mai kwanan wata 9 ga Oktoba, 2026, majalisar ta ce shugaban hukumar ya shafe shekaru takwas a jere yana kan muƙaminsa, cewar The Sun.

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Tsohon Shugaban FRSC ta Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

Hukumar alhazai: Malamai sun rubuta wasika ga Gwamna

Malaman sun bayyana cewa hakan ya sa Isola ya zama shugaban da ya fi kowa daɗewa a wannan muƙami tun lokacin da aka kafa hukumar.

Wasiƙar, wadda mai kula da ayyukan ƙungiyar a jihar, Malam Isiak Abdul Rahman, da wasu malaman Musulunci biyar suka sanya wa hannu, ta ƙunshi wakilan yankunan Ede, Ikire, Ife, Ikirun da Ila Orangun.

Ƙungiyar ta ce babu wani dalili da zai sa a sake bai wa Isola wani wa’adin shugabanci bayan ya shafe tsawon lokacin da aka saba yi a muƙamin.

Malaman sun bayyana hakan ne yayin mayar da martani ga wata sanarwar haɗin gwiwa da Osun State League of Imams and Alfas ta fitar, inda ta nemi a tsawaita wa’adin shugabancin Isola.

Sun ce tsawaita wa’adin ko sake naɗa shi ba zai amfani hukumar ba, kuma hakan zai iya hana sauran yankuna samun damar shugabantar hukumar.

Kara karanta wannan

Shettima ya magantu a kan tsoron da 'yan Arewa ke ji kan tazarcen Tinubu

Malamai sun tura wasika ga gwamna kan shugaban hukumar alhazai
Taswirar jihar Osun da ake takaddama kan kujerar shugaban alhazai. Hoto: Legit.
Source: Original

Musabbabin adawar da malaman ke yi

Ƙungiyar limaman ta ce babu wani yanki da zai iya ɗaukar muƙamin a matsayin nasa shi kaɗai, tana mai cewa yankunan Ede, Ife, Ikire da Ikirun ba su taɓa samar da shugaban hukumar ba.

Sai dai ƙungiyar ta ce ya kamata a yi la’akari da adalci wajen raba muƙamin ne bayan wa’adin Isola ya ƙare a shekarar 2030, cewar Punch.

A nata martanin, majalisar malamai ta bayyana hasashen tsawaita wa’adin zuwa 2030 a matsayin rashin adalci da wuce gona da iri, domin hakan zai sa Isola ya shafe shekaru 12 a muƙamin.

Majalisar ta ce:

“Duk wani yunƙuri na tsawaita wa’adinsa bayan wannan shekara ta 2026 zai sa ya shafe shekaru 12 yana shugaban hukumar jin daɗin alhazai, abin da bai taɓa faruwa a kowace jiha a Kudu maso Yamma ba.
Babu wanda ya taɓa shafe fiye da shekaru takwas a matsayin shugaban hukumar a jihohin yankin.”

Kara karanta wannan

Zaɓen 2027: Kashim Shettima ya shiga ganawar sirri da tsofaffin gwamnoni

Osun: Musulmi da Kirista sun dauki matakan tsaro

Kun ji cewa hukumar DSS ta yi gargadi kan wani shirin kai hari wuraren ibada a Osun, lamarin da ya sa Kiristoci da Musulmi suka ɗauki matakan tsaro.

Kungiyar CAN ta umurci coci-coci su ƙarfafa tsaro tare da binciken baƙin da ke ziyartar wuraren ibada.

Ƙungiyar Musulmin Osun ta bi sahun CAN, inda ta buƙaci limamai su ƙara sa ido kan baƙi da kuma sanar da hukumomin tsaro duk wani motsi da ake zargi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.