Gwamnatin Najeriya
Bayan kammala taronta na kwanaki biyu, majalisar zartarwar tarayya (FEC) ta amince da wasu muhimman tsare-tsare da ayyuka da za su kara habaka tattalin arzikin kasa.
Babban bulaliyar majalisar dattawa, Ali Ndume ya bayyana cewa zai goyi bayan hukuncin kisa ga wadanda suka saci Ntrn amma ya nemi a kyale barayin N1m da N1bn.
Hukumomi a jihar Lagos sun dauki gagarumin aikin tsaftace gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba a yankin Lekki. Ana ganin hakan zai taimaka wajen tsaftace jihar.
A yayin da matsalar tsaro ke kara ci wa gwamnati tuwo a kwarya, Ministan tsaro, Mohammed Badaru ya yi kira ga kungiyar tarayyar Turai da ta tallafawa Nigeria.
Bayanai sun nuna ‘Yan majalisar Najeriya za su tashi da kusan Naira biliyan 50 daga cikin baitul-mali a shekarar 2024 a matsayin albashi da alawus.
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya zargi tsohon gwamnan jihar Nyesom Wike da ciwo basussukan da su ka kai biliyoyin Naira, inda yan kwangila ke neman a biya.
A yau ne gwamnatin tarayya za ta kaddamar da gina dakunan kwanan dalibai a manyan makarantu 12 a fadin kasar nan, inda za a fara da jami’ar jihar Akwa Ibom.
Mambobin kungiyar shugabannin mata na jam’iyyar APC na jihohi 37 da Abuja, sun koka kan yadda Shugaba Bola Tinubu ya ki tunawa da su a rabon mukaman siyasa.
Akwai yiwuwar gwamnatin tarayya ta samar da kwarya-kwaryan kasafi matukar za ta biya karin albashin ma’aikata da kungiyoyin kwadago ke ta fafutukar a yi.
Gwamnatin Najeriya
Samu kari