"N48,000 Tayin Almajirai Ne”: Shehu Sani Ya Caccaki Gwamnati Kan Mafi Karancin Albashi

"N48,000 Tayin Almajirai Ne”: Shehu Sani Ya Caccaki Gwamnati Kan Mafi Karancin Albashi

  • Sanata Shehu Sani ya ya caccaki gwamnatin tarayya kan mafi karancin albashi na Naira 48,000 da ta gabatarwa 'yan kwadago
  • Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, ya ce tayin almajirai ne gwamnatin tarayyar ta yi wa 'yan kwadago, duk da cewa motsi yafi labewa
  • Idan ba a manta ba, 'yan kwadago da gwamnatin tarayya sun tashi baram-baram a taron da suka yi a ranar Laraba kan albashin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya caccaki gwamnatin tarayya kan mafi karancin albashi na N48,000 da ta gabatarwa 'yan kwadago.

Shehu Sani ya yi magana kan mafi karancin albashi
Shehu Sani ya goyi bayan 'yan kwadago kan mafi karancin albashi. Hoto: @ShehuSani
Asali: Facebook

Legit Hausa ta ruwaito cewa kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun yi watsi da N48,000 da gwamnatin tarayya ta gabatar a matsayin mafi karancin albashi.

Kara karanta wannan

Dan majalisar PDP ya nemi Tinubu ya fara tafiye tafiye a mota ko ya hau jirgin haya

"Tayin albashin almajirai gwamnati tayi" - Sanata

Shehu Sani, a ranar Alhamis, 16 ga Mayu ya wallafa a shafinsa na X cewa, "tayin almajirai gwamnati ta yi wa 'yan kwadago."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"To amma dai, motsi ai ya fi labewa."

Albashi: 'Yan kwadago sun fusata da gwamnati

Gwamnatin tarayya ta bayar da shawarar biyan N48,000 matsayin mafi karancin albashin a yayin taron kwamitin albashi da 'yan kwadago a ranar Laraba.

Cikin fushi, 'yan kwadago suka fice daga taron, wanda aka gudanar a yanar gizo, lamarin da ya sa ba a wani cimma wata matsaya kwakkwara ba.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero da mataimakin shugaban TUC, Kwamared Tommy Okon sun fitar da sanarwa guda daya bayan taron.

Kungiyoyin kwadagon sun nuna cewa N48,000 da gwamnatin ta gabatar tamkar cin fuska ne tare da wulakanta ma'aikatan kasar.

Kara karanta wannan

"Ba ka da lissafi ko kadan": Kungiyar TUC ta ɗaga yatsa ga Tinubu kan karin albashi

An daga yatsa ga Tinubu kan albashi

Tun da fari, mun ruwaito cewa kungiyar 'yan kasuwa ta TUC ta daga yatsa ga Shugaba Bola Tinubu tana mai cewa babu hankali a N48,000 da gwamnati ta gabatar matsayin mafi karancin albashi.

Shugaban kungiyar, Festus Osifo wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba 15 ga watan Mayu inda ya nemi gwamnati ta kawo tsarin da N48,000 za ta ishi ma'aikaci a kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.