“Yan Siyasa Na Satar Kudi ne Domin Su Rabawa Talakawa”, Sanata Ndume Ya Fasa Kwai

“Yan Siyasa Na Satar Kudi ne Domin Su Rabawa Talakawa”, Sanata Ndume Ya Fasa Kwai

  • Babban bulaliyar majalisar dattawa, Ali Ndume, ya bayyana cewa zai goyi bayan hukuncin kisa ga wadanda suka saci Naira tiriliyan daya
  • Sai dai Sanata Ali Ndume ya ce bai kamata a yi wa 'yan siyasar da ke satar Naira miliyan ko biliyan daya hukunci mai tsanani ba
  • Bulaliyar majalisar ya yi nuni da cewa 'yan siyasa na satar kudin ne domin rabawa da jama'a yayin da ya amince a kashe masu fataucin kwayoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Babban bulaliyar majalisar dattawa, Ali Ndume, ya bayyana banbancin cin hanci da rashawa na ‘yan siyasa da sauran mutane gama-gari.

Sanata Ndume ya ce 'yan siyasar Najeriya na satar kudi ne saboda su rabawa mutane, don haka laifin ba nasu ne kadai ba, bai ma kamata a yi masu hukunci mai tsanani ba.

Kara karanta wannan

Kakakin majalisar jihar Niger zai aurar da marayu 100

Sanata Ali Ndume ya yi magana kan 'yan siyasa da ke satar kudin jama'a
Sanata Ali Ndume ya nemi a yi wa 'yan siyasa da ke satar N1m zuwa N1bn sassauci. Hoto: @Imranmuhdz
Asali: UGC

"A hukunta barayin N1trn" - Ndume

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Sanata Ndume ya yarda cewa 'yan siyasa suna "satar kudi domin su raba tare da mutane".

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bulaliyar majalisar, ya kuma bayyana cewa zai goyi bayan hukuncin kisa ga wadanda suka saci Naira tiriliyan daya, yana mai gargadin cewa ka da a kashe barayin Naira milyan ko biliyan daya.

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata lokacin da ya ke tattaunawa da gidan talabijin na Channels TV, inda ya yi magana kan hukuncin kisa ga masu safarar miyagun kwayoyi.

"Yan siyasa na satar kudi" - Ndume

A cewar Ndume:

“Mu 'yan siyasa ba ma yin kwanmu sai da zakara. Muna satar kudi ne mu je mu raba da jama'a, domin idan ba ka ba su ba, to ba za ka koma zauren majalisar ba.

Kara karanta wannan

InnalilLahi: 'Yan bindiga sun bindige ma'aikacin FIRS a tsakiyar birnin Abuja

"Idan har za a yanke hukuncin kisa ga barayin gwamnati, zan goyi baya amma ka da a kashe masu satar Naira miliyan ko biliyan daya, amma wanda ya saci Naira tiriliyan daya a kashe shi."

Sanata Ndume ya ce yana goyon bayan a yanke hukuncin kisa ga masu safarar miyagun kwayoyi domin suna kashe al'uma ne gaba daya, in ji rahoton Vanguard.

Majalisa za ta zartar da dokar kisa

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Majalisar dattijai ta zartar da wani kudiri na dokar hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (da aka sabunta) 2024.

Kudirin ya tanadi hukuncin kisa ga mutanen da aka samu da laifin yin fataucin miyagun kwayoyi da sauyan kayan maye.

To sai dai kuma masu ruwa da tsaki da dama sun tafka muhawara da a kan kudurin, inda wasu ke ganin bai kamata shugaba Bola Tinubu tabbatar da shi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel