Ana Tsaka da Binciken TETFund, an Fitar da N1bn a Sharewa Dalibai Hawaye a Makarantu

Ana Tsaka da Binciken TETFund, an Fitar da N1bn a Sharewa Dalibai Hawaye a Makarantu

  • Gwamnatin tarayya za ta kashe Naira biliyan 1 wajen gina dakunan kwanan dalibai 12 a jami'o'i da kwalejoji guda 12 da aka zaba
  • Da ya ke sanar da hakan, shugaban TETFund, Sonny Echono ya ce dalibai na samun nakasu a karatu saboda dakunan kwana marasa kyau
  • Wannan dai na zuwa ne yayin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ke binciken TETFund kan badakalar kwangiloli

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta amince da fitar da N1bn gina dakunan kwanan dalibai a manyan makarantu 12 da suka kunshi jami’o’i shida, kwalejojin fasaha uku da kwalejojin ilimi uku.

Gwamnatin tarayya ta sanar da amincewar fitar da kudin ne a matsayin gudummawar hannun jari a hadin gwiwarta da 'yan kasuwa a harkar gini.

Kara karanta wannan

"Wannan ai sata ce," NLC ta magantu kan karin kudin wutar lantari a Kogi

Gwamnati za ta fara gina dakunan kwanan dalibai a manyan makarantu
Gwamnatin tarayya ta ware N1bn domin gina dakunan kwanan dalibai a jami'o'i da kwalejoji. Hoto: @TETFundNg
Asali: Twitter

Dalilin gina dakunan dalibai a makarantu - TETFund

An sanar da hakan ne a wajen wani taron karawa juna sani kan ‘Abubuwan da dalibai ke bukatu a manyan makarantu’ wanda hukumar TETFund ta shirya a Abuja ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Talabijin na Channels, ya ruwaito shugaban hukumar, Sonny Echono, ya ce mummunan yanayin dakunan kwanan dalibai a manyan makarantun na kawo cikas ga karantun daliban.

Har ila yau, Echono ya bukaci shugabannin makarantun ilimi da su samar da sabbin hanyoyin ba da horo ga malamai domin cimma muradin gwamnatin tarayya kan hakan.

Aikin gina dakunan zai fara a Akwa Ibom

"Ina mai farin cikin sanar da ku cewa, Africa Plus Partners, tare da hadin gwiwar jami'ar jihar Akwa Ibom, za su kaddamar da ginin dakunan kwanan dalibai ta hanyar tallafin TETFund

Kara karanta wannan

Wahalar Rayuwa: Ka da a Karaya da Mulkin Bola Tinubu, Jigon APC Ya Lallabi Mutane

“A yayin da dakunan kwanan dalibai suka yi kadan, mun kuma lura cewa yawancinsu suna cikin mawuyacin hali, musamman game da karkon gini aiki da tsafta."

-A cewar Echono, kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

ICPC ta kama daraktar TETFund

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta soma wani bincike a hukumar TETFund kan zargin an yi badakalar kwangilar Naira biliyan 3.8.

A yayin da take binciken, an ce ICPC ta tsare Gloria Olotu, daraktar kudi da kula da asusu ta hukumar tallafawa manyan makarantun bayan yi mata tambayiyi.

Wata majiya daga hukumar ICPC ta ce ana zargin Gloria Olotu da sa hannu a kwangilar da TETFund ta ba makarantar Fides Et Ratio wanda ya sabawa doka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel