Hukumar FIRS Ta Tara Naira Tiriliyan 3.94 a Watanni 3, Ta Fadi Biliyoyin da Take Hari a 2024

Hukumar FIRS Ta Tara Naira Tiriliyan 3.94 a Watanni 3, Ta Fadi Biliyoyin da Take Hari a 2024

  • Daga farkon watan Janairu zuwa karshen watan Maris, hukumar FIRS ta bayyana cewa ta tara Naira tiriliyan 3.94 na kudin haraji
  • Shugaban FIRS, Zacch Adedeji ne ya bayyana adadin kudin a ranar Alhamis inda ya ce suna son tara Naira tiriliyan 19.4 a 2024
  • Mista Adedeji ya bayyana haka ne a yayin da shugabannin hukumar CRMI suka kai ziyara zuwa hedikwatar FIRS da ke Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar tara haraji ta kasa FIRS ta ce ta tara kudaden haraji na Naira tiriliyan 3.94 a cikin watanni uku na farkon shekarar 2024 (Q1).

Shugaban hukumar FIRS, Zacch Adedeji ne ya bayyana adadin kudaden a ranar 15 ga watan Mayun 2024.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: EFCC ta na neman gwamnan PDP ruwa a jallo? Gaskiya ta fito

Hukumar FIRS ta yi magana kan kudin da ta tara
2024: Hukumar FIRS ta tara N3.94trn a watanni 3. Hoto: @FIRSNigeria
Asali: Twitter

FIRS ta gaza tara N4.8trn a wata 3

Jaridar The Cable ta ruwaito kudin ya yi kasa da Naira Tiriliyan 4.8 da hukumar ta sa ran tarawa a duk bayan watanni uku har shekarar ta kare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adedeji ya bayyana haka ne a yayin wata ziyarar ban girma da shugabannin hukumar CRMI, karkashin jagorancin Ezekiel Oseni, suka kai hedkwatar FIRS da ke Abuja.

Ya ce kudin da aka tara a farkon 2024 ya zarce wanda aka samu a farkon 2023 da kashi 56.7, kamar yadda rahoton Arise TV ya nuna.

'Ana burin tara N19.4trn a 2024' - FIRS

Musta Adedeji wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan hukumarsa, Mista Tayo Koleosho a wajen taron, ya ce yana da burin tara Naira tiriliyan 19.4 a shekarar 2024.

A cewar Adedeji:

“A cikin shekarun da suka gabata karkashin gwamnatoci daban-daban, hukumar FIRS ta kasance ta na gudanar da ayyukanta na tara kudaden shiga tare da cimma muradin gwamnati."

Kara karanta wannan

Aiki ba lasisi: Kotu ta yanke hukuncin dauri kan 'yan canji 17 da aka kama a Kano

Dalla-dalla: Albashin 'yan majalisar Nigeria

A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar dattawa, wakilai da ta jihohi 36 tare da hukumomin da ke karkashin su za su kashe kimanin N720bn a 2024.

Wannan kudin ya shafi albashin 'yan majalisar da alawus dinsu da kuma na ma'aikatan da ke karkashin su kamar yadda muka yi bayani dalla-dalla kan yadda za a kashe kudin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel