"Tsohon Gwamna Nyesom Wike ya Tarawa Ribas Bashi," Simi Fubara Ya Fasa Kwai

"Tsohon Gwamna Nyesom Wike ya Tarawa Ribas Bashi," Simi Fubara Ya Fasa Kwai

  • Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya zargi tsohuwar gwamnatin da Nyesom Wike ya jagoranta da tarawa jihar tilin bashi na ayyukan da aka aiwatar
  • Gwamnan ya bayyana cewa yanzu haka 'yan kwangila sun addabi gwamnatinsa da neman cikon kudin aikin da suka aiwatar a kan bashi
  • Wannan furuci dai zai kara ta'azzara matsalar da ke tsakanin shugabannin biyu, domin ko a yanzu Gwamnan ya kafa kwamitin da zai binciki mulkin Wike

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Rivers- Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa tsohon gwamna Nyesom Wike ta tarawa jihar tulin bashi.

Ya ce yanzu haka ‘yan kwangila su na ta neman gwamnatinsa ta biya cikon kudin kwangilar ayyukan da su ka aiwatar wanda ya kai biliyoyin Naira.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: EFCC ta na neman gwamnan PDP ruwa a jallo? Gaskiya ta fito

Nyesom Wike
Gwamna Siminalayi Fubara na zargin Nyesom Wike da tarawa jihar Rivers bashi Hoto: Nyesom Ezenwo Wike/Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Da bashi Wike ya yi ayyuka a Ribas?

Punch News ta wallafa cewa tsohon Gwamna Nyesom Wike ya shahara wajen kaddamar da ayyuka, ciki har da titunan sama da guda 12.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yawan ayyukan da tsohon Gwamnan ke aiwatarwa har ya sanya ake kiransa da ‘Mr. Projects' watau Mai ayyuka.

Gwamna Fubara zai bincike mulkin Wike

Gwamnan jihar Rivers, Siminilayi Fubara ya bayyana takaicin yadda ‘yan kwangila da yawa su ka damu gwamnatinsa wajen neman cikon kudin aikin da su ka aiwatar a mulkin Nyesom Wike.

Kan haka ma ya kafa kwamitin da zai binciki yadda tsohuwar gwamnatin ta gudanar da ayyukanta, lamarin da wasu ke ganin hakan bita da kulli ce kawai, kamar yadda The Guardian ta wallafa.

Tsohon Sanata, Olaka Nwogu ya shaidawa Gwamnan Smininalayi Fubara cewa irin wannan bibiyar da ya ke yiwa tsohon gwamnan zai kara zurfafa gaba da kiyayyar da ke tsakaninsu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: 'Rashin tsaro a Arewa zai haifar da babbar fitina a yammacin Afrika', gwamna

EFCC da neman Gwamna Fubara

Mun kawo muku labarin cewa hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) ta yi karin haske kan rahotannin da ke cewa ta na neman gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ruwa a jallo, kamar yadda ake yadawa.

Sai dai a binciken kwa-kwaf da Legit Hausa ta yi an gano labarin a matsayin tsagwaron karya domin EFCC ba ta neman Gwamna Siminalayi Fubara a wannan lokaci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel