Gwamnatin Najeriya
Hukumar asusun NELFund ta sanar da cewa ta dakatar da ba daliban manyan makarantu mallakin jihohi damar neman rancen kudin karatu har na tsawon mako 2.
Kungiyar SEPAP ta bukaci bankin duniya ya binciki gwamnatin tarayya da jihohi kan yadda suke kashe bashin da suka ciwo wanda galibi bai amfanin talakawan kasar.
Hukumar sadarwa ta Najeriya NCC ta ce kashi 100 na katin SIM da ake amfani da su a kasar nan ana yin su ne a cikin gida. NCC ta yi magana kan shirin NORDIT.
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP, Peter Obi ya caccaki yadda shugaba Bola Ahmed Tinubu ke nuna halin ko-in-kula da talakan Najeriya ke ciki.
Ofishin kula da basussuka (DMO) ya bayyana cewa an samu raguwar basussukan cikin gida da jihohin kasar nan 35 suka karba a watanni ukun farko na 2024.
Jigon jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya bayyana Janar Sani Abacha a matsayin mafi kyawun shugaban kasar Najeriya idan aka kwatanta da sauran da aka taba yi.
Matsakaicin farashin man fetur a watan Mayun 2024 ya kai N769.62, wanda ke nuni da karuwa idan aka kwatanta da farashin da aka saye shi a watan Mayun 2023 (N238.11).
Kungiyoyin ma’aikatan jami’o’in Najeriya sun ba gwamnatin tarayya wa’adin mako biyu da ta biya su albashin watanni hudu da ta rike ko ta fuskanci fushin kungiyoyin.
Bankin duniya ya kafawa Najeriya manyan sharudda kafin ya ba ta rancen dala biliyan 1.5. Bankin Duniya ya ce zai iya soke rancen kudin idan aka karya dokokin.
Gwamnatin Najeriya
Samu kari