"Kalamanka ba Su Dace da Shugaba Ba," Peter Obi ya Caccaki Tinubu kan Talauci a Najeriya

"Kalamanka ba Su Dace da Shugaba Ba," Peter Obi ya Caccaki Tinubu kan Talauci a Najeriya

  • Dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi ya caccaki Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ke cewa ba a Najeriya ne kawai ake shan wahala ba
  • Mista Obi ya ce kalaman ba su dace su fito daga bakin shugaban kasa da ake fatan zai kawo gyara da sauki cikin tarin matsalolin da ‘yan kasar suke ciki ba
  • 'Dan takaran na jam’iyyar LP yana ganin abin da ya fi dacewa shi ne gwamnatin tarayya ta gaggauta lalubo hanyoyin kawo gyara ko ‘yan kasa za su ji sauki-sauki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- 'Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP, Peter Obi ya caccaki yadda shugaba Bola Ahmed Tinubu ke nuna halin ko-in-kula da talakan Najeriya ke ciki.

Kara karanta wannan

Mahara sun dira Jihar Binuwai a babur, an shiga fargaba bayan kashe rayuka

Peter Obi yana ganin kamata ya yi shugaba Tinubu ya mayar da hankali kan yadda kasar nan za ta fita da halin da take ciki ba wai nuna cewa ba talakawan kasar ne kadai ke cikin wahala ba.

Tinubu
Peter Obi ya zaburar da Shugaba Tinubu kan warware matsalolin Najeriya Hoto: Mr. Peter Obi/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A jerin sakonnin da dan takarar a zaben 2023 ya wallafa a shafinsa na X, Obi ya ce ba abu ne mai kyau ba a ji shugaban da ya kamata ya taimaki jama’arsa na fadin cewa ai ba su kadai suke wahala ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A Najeriya talauci ya fi katutu” - Obi

'Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP a zaben da ya wuce, Peter Obi ya ce babu kasar da ke fama da talauci a duniya sama da Najeriya.

Nigerian Tribune ta wallafa cewa Najeriya ke jagorancin sauran kasashe ta fuskoki da dama ciki har da yawan yara marasa zuwa makaranta, talauci, yunwa da rashin ingantaccen ilimi.

Kara karanta wannan

PDP ta tsoma baki kan rikicin Ribas, yayin da APC ke neman a sanya dokar ta baci

Mista Obi ya kara da cewa tarin matsalolin da kasar ke fuskanta ya sa ya wajaba kan gwamnatin Tinubu ta lalubo hanyoyin magancesu da fitar da al’umma daga kangin rayuwa.

“Duk duniya ne ake talauci,” Tinubu

A wani labarin kun ji shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce talauci da kuncin rayuwa da ake fuskanta ba iya Najeriya ba ne, haka ake ji a sauran kasashen duniya.

Shugaban ya fadi haka ne lokacin ziyarar tawagar ‘yan majalisar kasar nan, karkashin jagorancin Godswill Apkabio da mataimakinsa Barau Jibrin suka kai masa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.