Hukumar NCC Ta Bayyana Inda Ake Ƙera Layukan Wayan da Ƴan Najeriya Ke Amfani da Su

Hukumar NCC Ta Bayyana Inda Ake Ƙera Layukan Wayan da Ƴan Najeriya Ke Amfani da Su

  • Hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ce kashi 100 na layukan wayoyi da ake amfani da su a ƙasar ana hada su ne a nan cikin gida
  • Shekaru biyu da suka gabata, NCC ta ce ana shigo da dukkanin layukan da ake amfani da su, amma yanzu hakan ya zama tarihi
  • NCC ta ce ta hanyar amfani da shirin hukumar na NORDIT ya taimaka wajen tallafawa kamfanonin da basussuka domin su ci gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ce kashi 100 na layukan wayoyi (SIMs) da ake amfani da su a kasar nan ana yin su ne a cikin gida.

Kara karanta wannan

Zambar Naira miliyan 22: EFCC ta cafke ma'aikacin karya a fadar shugaban kasa

Shugaban shashen kafafen yada labarai na NCC, Injiniya Babagana Digima, ya bayyana hakan a wani horon da aka yi wa ma'aikatan hukumar na shashen yada labaran a Legas.

NCC ta yi magana kan layukan wayoyi da ake amfani da su a Najeriya
NCC ta bayyana cewa ana hada kashi 100 na layukan da ake amfani da su a cikin gida. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa horon na kwana biyu an yi masa take da: "Horas da masu ruwa da tsaki a harkar sabbin kafofin sada zumunta kan bunkasa sadarwa."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A Najeriya ake hada layuka" - NCC

Shugaban sashen ya ce:

"Sashe na 1D har zuwa F na dokar hukumar NCC ya yi bayani kan karfafa amfani kamfanonin sadarwa na cikin gida wajen bunkasa masana'antun ƙasar.
"A shekaru biyu da suka gabata, kusan kashi 99 zuwa 100 na layukan waya da ake amfani da su ana shigo da su ne daga kasar waje.
"Amma lokacin da muka kaddamar da sashen NORDIT, mun umarci dukkanin kamfanonin kamfanonin sadarwa (MNOs) su rika hada layukansu a cikin gida, kuma an cimma hakan."

Kara karanta wannan

EFCC ta gurfanar da ma'aikacin gwamnati gaban Kotu saboda zargin hana bincike

Amfani da NORDIT wajen bunkasa kamfanoni

Digima, wanda shi ne tsohon shugaban NORDIT, ya yi nuni da cewa ta hanyar NORDIT, an cusa kamfanonin cikin gida wajen shirye shiryen sadarwa na gwamnatin kasar.

Ya ce NORDIT ta taimaka wa kamfanoni da dama da basussuka domin ganin sun bunkasa a harkar masana'antu a kasar, in ji rahoton jaridar The Guardian.

An yi jana'izar mahaifin Sanata Munguno

A wani labarin, mun ruwaito cewa, mahaifin sanatan Borno ta Arewa, Mohammed Tahir Munguno, Alhaji Tijjani Muhammad ya rigamu gidan gaskiya.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa jana'izar Alhaji Tijjani, wanda aka yi masa sutura a yau Lahadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.