Albashi: Gwamnati Ta Fusata Ma’aikatan Jami’o’i, Sun ba Tinubu Wa'adin Mako 2

Albashi: Gwamnati Ta Fusata Ma’aikatan Jami’o’i, Sun ba Tinubu Wa'adin Mako 2

  • Da yiwuwar kungiyoyin ma'aikatan jami'o'in Najeriya su tsunduma yajin aiki nan da mako biyu bayan aika wa gwamnati wasika
  • Kungiyoyin NASU da SSANU sun sha alwashin rufe jami'o'in da ke fadin kasar saboda gwamnati ta rike albashin 'ya 'yansu
  • Ma'aikatan sun nemi gwamnatin ta biya albashin nan da mako biyu ko kuma ta ga fushinta a zahirance wanda zai hada da rufe jami'o'in

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyoyin ma’aikatan jami'o'in Najeriya na NASU da SSANU sun ba gwamnatin tarayya wa’adin mako biyu domin biyan albashin mambobinsu na wata hudu.

Kungiyoyin sun sha alwashin rufe jami'o'in da ke fadin kasar idan gwamnati ta gaza biyan albashin da aka rikewa ma'aikatan ta idan wa'adin ya kare.

Kara karanta wannan

Musulmi na murnar Sallah, mazauna Kano na bakin cikin kwace gonakinsu

Ma'aikatan jami'o'i sun aikawa gwamnati wasika
Kungiyoyin NASU da SSANU sun yi barazanar rufe jami'o'in Najeriya. Hoto: @SSANU_NATIONAL.
Asali: Twitter

NASU, SSANU sun aikawa gwamnati wasika

A wata wasika da suka aikewa ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman, SSANU da NASU sun zargi gwamnati da sakaci da kuma rashin gaskiya, in ji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasikar mai taken: “Rike albashin wata hudu: Bukatar biya cikin gaggawa,” ta samu sa hannun babban sakataren NASU, Prince Peters Adeyemi da shugaban SSANU, Comrade Mohammed Ibrahim.

Kungiyoyin sun ce ba za su ce za su iya shiga yajin aiki a dukkanin fadin kasar ma damar gwamnati ta gaza biyan mambobinta albashin da suke bi.

Ma'aikatan jami'o'in gwamnati na barazanar yajin aiki

Kungiyoyin kwadagon wadanda suka zargi gwamnati da yin watsi da duk wani tayi na zaman sulhu sun ce:

“Shirun da gwamnati ta yi da kuma rashin biyan albashin da aka rike yana haifar da harzuka da cece-kuce a tsakanin mambobinmu a Jami’o’in kasar.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Sarki Sanusi ya tura sakwanni biyu ga Kanawa a ranar sallah

“Saboda haka muna bukatar a gaggauta biyan mambobinmu albashin watanni hudu da aka hana su nan da mako biyu (2) ko kuma mu rufe gaba daya jami'o'in kasar."

An soke kananan hukumomi a Ondo

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata babbar kotun jiha ta rusa dokar da ta kirkiri karin kananan hukumomi 33 a jihar Ondo.

Alkalin kotun, Adegboyega Adebusoye, ya ayyana kirkirar kananan hukumomin a matsayin abin da ya sabawa kundin tsarin mulki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.