Rahoton NBS: Jigawa da Jerin Jihohin Najeriya da Suka Fi Tsadar Man Fetur a Watan Mayu

Rahoton NBS: Jigawa da Jerin Jihohin Najeriya da Suka Fi Tsadar Man Fetur a Watan Mayu

  • Jigar Jigawa ce ta fi ko ina tsadar man fetur a Najeriya inda ake sayar da lita daya a kan N937.50 kamar yadda rahoto ya nuna
  • Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta ce mafi saukin farashin da 'yan Najeriya ke sayen litar man fetur ya karu zuwa N769.62
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wani manajan gidan man fetur da kuma ɗan bumburutu a jihar Kaduna kan yadda suke sayar da fetur a Mayu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta ce matsakaicin farashin da 'yan Najeriya ke sayen man fetur ya karu zuwa N769.62 kan kowace lita a watan Mayun 2024.

Kara karanta wannan

DMO: Jihohi sun rage karbo bashin gida yayin da kudin da ake bin Najeriya ya karu

A rahoton farashin fetur da ta saki a ranar Alhamis, NBS ta ce an samu karuwar kudin da kashi 223.21 idan aka kwatanta da N238.11 da aka sayar da kowacce lita a Mayun 2023.

Hukumar NBS ta yi magana kan farashin fetur
Hukumar NBS ta fitar da rahoton farashin fetur na watan Mayun 2024. Hoto: @officialABAT
Asali: Getty Images

Farashin man fetur ya tashi da 9.75%

Haka kuma, idan aka kwatanta farashin da na watan da ya gabata (watau Afrilun 2024), matsakaicin farashin lita daya ya karu da kashi 9.75% daga N701.24.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar NBS ta wallafa rahoton farashin ne a shafinta na intanet a makon nan.

Jihohin da suka fi tsadar fetur

Hukumar ta ce a nazarin farashin fetur a jihohi, an gano cewa ana sayar da lita kan N937.50 a jihar Jigawa, a Ondo kuma lita ta kai N882.67 yayin da ake sayar da lita kan N882.22 a jihar Benue.

Kara karanta wannan

Rahoton DMO: Bashin da ake bin Najeriya ya ƙaru da Naira tiriliyan 24 cikin wata 3 kacal

Hukumar ta kuma ce an samu saukin farashin litar fetur a jihar Legas, inda ake sayar da ita kan N636.80, sai Nija a kan N642.16 da kuma Kwara a kan N645.15.

NBS ta ce yankin Arewa maso Yamma ne ke da mafi tsadar fetur a kan N845.26, yayin da Arewa ta tsakiya ke da mafi saukin farashi a kan N695.04 kan kowacce lita.

Farashin litar fetur a jihar Kaduna

A zantawar Legit Hausa da wani manajan gidan man Shade Gas & Petrol Ltd, Kaduna, ya ce yanzu suna sayar da litar man fetur a kan N765.50, yayin da suka gaza kawo gas saboda tsadar da ya yi.

Manajan gidan man ya ce farashin man na da alaƙa ne da yadda aka canja Naira a kan dalar Amurka, domin farashin na haurawa idan dala ta tashi, ko ya sauko idan Naira ta tashi.

Dangane da yanayin kasuwar, manajan ya ce haka nan mutane ke sayen man duk da tsadar dashi, amma yana fatan nan gaba kaɗan farashin zai sauka zuwa kasa da N700/L.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a Ado Bayero Mall a Kano, har yanzu ana kokarin kashe wutar

Haka zalika, mun zanta da wani dan bumburutu, Hassan Mai Fetur, wanda ya ce suna sayar da kwatar jarka a kan N1,000 yayin da galan mai cin lita hudu ya koma N4,000.

Bankin duniya ya kafawa Tinubu sharudda

A wani labarin, mun ruwaito cewa Bankin Duniya ya bayyana dalilan da ka iya sawa ya soke rancen dala biliyan 1.5 da ya shirya ba Najeriya.

Kamar yadda wani rahoto ya nuna, akwai wasu sharudda da bankin ya kafawa Najeriya wanda idan ta gaza bin su zai sa ta rasa damar karbar kudin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.