“Dalilai 5 da Suka Sanya Abacha Ya Fi Sauran Shugabannin Najeriya Nagarta”

“Dalilai 5 da Suka Sanya Abacha Ya Fi Sauran Shugabannin Najeriya Nagarta”

Yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da korafi kan shugabancin Bola Tinubu, an bayyana marigayi Sani Abacha a matsayin mafi kyawun shugaban kasar kuma mai nagarta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jigon jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya yaba da salon mulkin tsohon shugaban kasar.

An jero dalilai 5 da suka sanya Abacha mafi kyawun shugaba a Najeriya
Buba Galdima ya ce Abacha yafi sauran shugabannin Najeriya nagarta. Zaynab Galadima.
Asali: Facebook

Buba Galadima ya jero dalilai biyar da yake ganin suka sa Sani Abacha yafi kowane shugaba da aka yi a kasar kyau, Tribune ta tattaro su.

Legit Hausa ta bankado dalilan Buba Galadima inda ya ke kora yabo ga marigayin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Abacha da farashin man fetur

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi, fitaccen Sarki mai daraja ya riga mu gidan gaskiya a Landan

Marigayi Janar Sani Abacha ya tabbatar da farashin mai ya tsaya cak ba tare da tashi ba har karshen mulkinsa.

Galadima ya ce hakan ya taimakawa 'yan kasuwa da sauran mutane wurin bunkasa tattalin arzikinsu.

2. Daidaituwar farashin Naira

Har karshen wa'adin mulkin Abacha na shekaru hudu, farashin dala ya kasance N84 wanda hakan ya taimakwa harkokin kasuwanci a kasar.

3. Manyan ayyukan cigaba lokacin Abacha

Janar Abacha ya samar da manyan ayyukan ci gaba a Najeriya da suka hada da gyaran sakatariyar Tarayya da ke Abuja.

Sauran sun hada da karasa ginin Majalisar Tarayya da gyara fadar shugaban kasa da sauransu.

4. Kau da kai ga dukiyar kasa

Marigayi Sani Abacha ya sha bamban da sauran shugabanni saboda taka tsan-tsan da dukiyar al'umma.

Galadima ya ce Abacha ko sisin kwabo bai sata ba daga dukiyar kasa sai dai ma ya saka tallafi a wurare da dama domin taimakon al'umma.

Kara karanta wannan

Mahara sun dira Jihar Binuwai a babur, an shiga fargaba bayan kashe rayuka

5. Dabarun adana kudin kasa

Abacha ya nemo dabarun adana kudin kasa domin shigo da wasu kayayyaki na musamman da za su amfani Najeriya.

Hakan ya taimaka wurin bunkasa tattalin arziki da kuma rage dogaro da karbo basuka a kasashen ketare.

Amma wani rahoto da BBC Hausa ta fitar a baya ya nuna yadda farashin fetur ya rika hawa da sauka a Najeriya, hakan ya faru har a lokacin Janar Sani Abacha.

Buba Galadima ya yabawa salon mulkin Abacha

A wani labarin, kun ji cewa jigon jam’iyyar NNPP, Buba Galadima ya bayyana cewa ba a taba samun nagartaccen shugaban kasa kamar Janar Sani Abacha ba.

Galadima wanda tsohon na hannun daman Muhammadu Buhari ne ya ce Abacha ko sisin kwabo bai dauka ba lokacin da ya ke mulki.

Ya ce tun da ake shugabannin soji na kasar Najeriya, Abacha har yanzu shi ne mafi nagarta da kasar ta yi a tarihi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.