Gwamnati Ta Gama Shirin Raba Buhuna Miliyan 1.4 Na Kayan Abinci a Jihohi - Minista

Gwamnati Ta Gama Shirin Raba Buhuna Miliyan 1.4 Na Kayan Abinci a Jihohi - Minista

  • Gwamnatin tarayya ta dage wajen ganin an raba buhunan kayan abinci ta yadda za a samu raguwar masu kukan yuwa
  • Ministan tattalin arzikin kasa, Olawale Edun ya shaida cewa za a fito da karin abinci a lokacin da ya yi jawabi a taron MoFI
  • Wale Edun ya nuna gwamnatin Bola Tinubu ba wasa take yi game da maganar yakar yunwa da karya farashin abinci ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Gwamnatin tarayya ta kammala shirye-shiryen fito da karin metric ton 60, 000 na hatsi domin ganin farashin abinci ya sauko.

Tsadar farashi da hauhawar kayan abinci ya sa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta dauki wannan mataki, This Nation ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta gaji, ta shirya binciken bashin N23tr da Emefiele ya ba gwamnatin Buhari

Abinci
Gwamnati za ta raba abinci Hoto: Getty Images/Buhari Sallau (Facebook)
Asali: UGC

Ministan tattalin arzikin Najeriya, Wale Edun ya bada wannan sanarwa a wajen wani taro da MoFI ya shirya ranar Talata a garin Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wale Edun ya ce gwamnatinsu ta Bola Tinubu da gaske take yi wajen taimaki marasa karfi kamar yadda jama’a su ke ta kiraye-kiraye.

Za a fito da buhunan abinci a Najeriya

Ministan yake cewa da farko shugaban kasa ya amince a fito da metric ton 42, 000 na hatsi, yanzu kuma za a kara da wasu metric ton 60, 000.

Kamar yadda Legit tayi lissafi, metric ton 60, 000 daidai yake da buhuna 1, 407,205.

Idan aka yi wannan, ana sa rai za a samu yalwa da saukin farashin kayan abinci a kasuwa. A yanzu ana kukan ana kwana da yuwa.

Abinci zai yi sauki a kasuwanni?

An rahoto Edun yana cewa shugaban kasa yana so abinci ya kai ga kowa, don haka za a bude rumbunan gwamnatin da ke fadin kasar.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun lalubo yadda Gwamnatin Buhari ta haddasa asarar Naira tiriliyan 17

Bayan nan, mahukunta sun dage wajen ganin kayan abinci ba su bar Najeriya zuwa kasashen ketare inda ‘yan kasuwa ke saidawa ba.

Gwamnatin Tinubu za ta farfado Naira

Rahoton This Day ya ce gwamnatin Tinubu tana bakin kokarinta wajen ganin an farfado da darajar Naira ganin Dala ta doshi N1900.

Shugaban MoFI, Dr. Armstrong Takang da shugaban majalisar da ke kula da kamfanin, Dr. Shamsudeen Usman ya yi bayani a taron.

Sanatoci za su binciki bashin CBN

Sai yanzu Sanatoci su ke cewa ba su san yadda aka yi da bashin da Muhammadu Buhari ya karbo ba, ana da labarin za su binciki bashin.

Bankin CBN ya ba gwamnatin tarayya aron kimanin N30tr a shekarun baya, majalisar dattawa za ta binciki yadda aka kashe kudin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel