Yanzu Nan: Mutane Sun Fasa Dakin Ajiya, An Sace Buhunan Abincin Gwamnati a Abuja

Yanzu Nan: Mutane Sun Fasa Dakin Ajiya, An Sace Buhunan Abincin Gwamnati a Abuja

  • Wasu ‘yan zauna-gari banza sun budewa mutane kofar sata bayan fasa dakunan ajiyan kaya da ke unguwar Gwagwa a birnin Abuja
  • Bayan an yi ta’adi a yankin, majiyoyi sun tabbatar da cewa mutane sun sace buhunan hatsi da sauran kayan abinci sun tsere da su
  • Jami’an tsaro ba su dauki mataki ba har barnar tayi kamari, kuma ana tsoron za a iya zuwa wasu dakunan ajiyan domin satar abinci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

FCT, Abuja - ‘Yan iskan gari sun fasa wurin ajiya na gwamnati da ke unguwar Gwagwa a birnin tarayya da ake fama da tsadar abinci.

Labarin da aka samu daga Daily Trust ya ce bayan wannan aika-aika da ya faru a safiyar Lahadin nan, an sace kayan abinci daga dakin.

Kara karanta wannan

Bayan Dangote, jama'a sun tare motar BUA, an wawushe kayan abinci ana tsakiyar yunwa

Abinci
Masu satar abinci kwanakin baya Hoto: Getty Images (Hoton nan bai da alaka da labarin yau)
Asali: Getty Images

Wasu mazauna birnin Abuja sun ce matasa ne suka yi dandazo, suka fasa dakunan ajiya da ke kusa da yankin Tasha a Gwagwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fasa dakunan abinci da sasafe

Lamarin ya faru da misalin karfe 7:00 na safiyar a lokacin da wasu suke sharan barci.

A sakamakon barnar da aka yi, mazauna unguwar nan sun ce matasan sun yi nasarar tserewa da buhunan masara da wasu hatsi.

Jaafar Aminu ya shaidawa jaridar cewa an kai har karfe 9:00 na safen yau ana satar kayan abincin, irin dai yadda aka yi a hanyar Zariya.

Makwabta sun zo satar abcinci

Malam Jaafar Aminu ya ce mutane daga makwabta kamar unguwannin Jiwa da Karmo sun rika durowa domin satar kayan abincin.

A sakamakon haka ne hanyar Gwagwa-Karmo ta cushe da safe nan. Titin ne ake bi domin zuwa yankunan Dei-Dei da Jabi a Abuja.

Kara karanta wannan

Mutane sun fusata, sun fito zanga-zanga kan hare-haren 'yan bindiga a jihar Arewa

Shi kan shi mutumin ya tabbatar da kurje jikinsa kafin ya samu ya bar wurin da aka yi barnar a lokacin da rayuwa take kara tsada.

Mazaunin Abuja ya ce babu abin da ba a sace ba

Christopher Agbo wanda ya ganewa idanunsa, ya ce ba a hatsi kurum aka tsaya ba. Kuma da alama za a sake fasa wasu wuraren.

Mutanen da suka yi wannan ta’asa sai da suka sace har karafunan da aka yi amfani da su wajen yin shinge a dakunan ajiyan.

Jami’an tsaro ta bakin kakakin rundunar Abuja, Josephine Adeh sun ce ana kokarin shawo kan lamarin a lokacin da aka kira ta.

Matsalar abinci da yunwa a jihohi

Rahoto ya tabbatar da maganganun da shugaban majalisar dattawa ya yi na rabawa gwamnonin jihohi N30bn ba gaskiya ba ne.

Godswill Akpabio ya ba gwamnoni hakuri a wani jawabi da Eseme Eyiboh ya fitar a Abuja a kan matsalar yunwa da ake ciki a yau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel