Aikin noma
Kayan abinci sun yi tsada a dalilin rashin samun taki, rashin kyawun noman damina, rufe iyaka da kokarin gwamnati ya sa musamman shinkafa za ta fi karfin talaka.
Ministan harkar wuta ya fito ya yi dogon bayani a game da durkushewar babban layin lantarki, Adebayo Adelabu ya ce matsala ce aka samu, hakan ya yi sanadiyyar cikas.
Hukumar Hasashen Yanayi (NiMet) ta ce za a tafka mamakon ruwan sama a Kano da Sakkwato, akasin Ondo, Edo, Delta, Bayelsa, Rivers, Imo, Akwa Ibom, Abia, Ebonyi.
Kungiyar Manoma a Najeriya (AFAN ) ta bayyana cewa wadanda su ka ci bashin kudaden lamuni na CBN yawanci ba manoma ba ne shi yasa samo kudaden zai yi wahala.
Yayin da barayi su ka yi yawa yanzu wurin satar amfanin gona, wasu manoma sun bayyana yadda su ke biyan kudi tare da kwana a gonaki don gudun satar kayan gona.
Wasu mutane sun kai farmaki rumbun abinci na gwamnati da ke jihar Bayelsa tare da dibar kaya masu tarin yawa, wani abincin ya rube a ajiye tun shekarar 2022.
Wasu magidanta na satar kayyayakin gonar mutane don kai wa iyalansu a jihar Taraba, wasu manoman sun ce ganin halin da ake ciki ba su kai su kara ba ga hukumomi
Za a ga tsadar abinci, buhun shikafa zai kuma tsada a kasuwa. ‘Yan kasuwan da ke Arewa a karkashin NACCIMA sun fara ankarar da al’umma kan halin da ake ciki
Gwamnatin Kano ta bankado wata badakalar makudan kudade a hukumar Samar da Kayan Noma, KASCO a jihar kan karkatar da Naira biliya 4 da aka ware don harkar noma.
Aikin noma
Samu kari