Tsadar Rayuwa: Tinubu Ya Tsaida Ranar Fara Rabon Abinci Tan Dubu 42 da Jihar da Za a Fara

Tsadar Rayuwa: Tinubu Ya Tsaida Ranar Fara Rabon Abinci Tan Dubu 42 da Jihar da Za a Fara

  • Yayin da ake yunwa a Najeriya, Gwamnatin Tarayya ta bayyana lokacin da za ta fara rabon kayan hatsi har tan dubu 42
  • Gwamna jihar Neja, Umar Bago shi ya bayyana haka bayan ganawa da Ministan Albarkatun Noma a Najeriya, Abubakar Kyari
  • Idan ba a manta ba, a kwankin baya, Shugaba Tinubu ya ware hatsi tan dubu 120 domin taimakawa ‘yan kasar da ke cikin wani hali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranar da za ta fara raba kayan hatsi tan dubu 42 da aka ware wa ‘yan kasa.

Gwamnatin ta ce zuwa mako mai kamawa gwamnatin za ta fara rabon hatsin daga jihar Neja a Arewacin Najeriya, Arise TV ta tattaro.

Kara karanta wannan

A fadi illar da Kiripto ke yi wa tattalin arziki yayin da aka cafke shugabannin Binance, za a haramta

Tinubu ya sanar da ranar fara rabon tan dubu 42 na abinci a Najeriya
Gwamnatin Tarayya za ta fara rabon kayan abinci a mako mai zuwa. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Yaushe Tinubu zai fara rabon kayan abincin?

Gwamnan jihar, Umar Bago shi ya bayyana haka bayan ganawa da Minsitan Albarkatun Noma, Abubakar Kyari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bago ya ce za su fara rabon kayan ne daga jihar Neja da ke Arewa maso Tsakiyar Najeriya a matsayin ta farko, cewar Tribune.

Gwamnan ya kuma ce a kokarinsa na taimakawa mutanen jihar, ya ware tirelar kayan abinci dubu 120 don rabawa kyauta.

Ministan Noma ya fadi hanyar rabon kayan

A bangarensa, Ministan Noma, Abubakar Kyari ya ce tan dubu 42 na masara da gero da gari za a raba su a dukkan fadin kasar.

Kyari ya ce rabon kayan noman rani karo na biyu za a fara rabawa a jihar a mako mai zuwa kafin kai wa ga sauran jihohi.

Domin tabbatar da an yi gaskiya, Ministan ya bada tabbacin cewa za a gudanar da aikin yadda ya dace ba tare da cuwa-cuwa ba.

Kara karanta wannan

Babban labari: Gwamnatin Najeriya ta cafke jami'an manhajar Binance, an samu ƙarin bayani

“Ina baku tabbacin cewa za a gudanar da rabon kayan yadda ya kamata, idan muka kammala tsarin raba kayan, kowa zai gani da kuma yadda za a yi.
“Mutane da dama sun damu kan abubuwan da suka faru a baya, amma za mu samar da yanayin yadda kowa zai gamsu.”

- Abubakar Kyari

Tinubu zai fara biyan matasa

Kun ji cewa Shugaba Tinubu ya yi alkawarin fara biyan matasa alawus domin rage musu radadin tsadar rayuwa.

Shugaban ya ce za a fara biyan ne ga matasa wadanda ba su da aikin yi musamman masu kwalin digiri da na Kwalejin Ilimi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel