Zaben Shugaban kasan Najeriya
A Taraba, Shugabannin Jam’iyyar Labour Party sun dakatar da Shugabar LP. Shugabar da aka dakatar daga ofis har na tsawon watanni 6 ta ce sharri ake yi mata
A jihar Neja, Asiwaju Bola Tinubu ya samu gudumuwar motoci da ofisoshin yakin neman zaben shugaban kasa daga wajen Sanata Sani Musa da Muhammad Idris Malagi.
Za a ji kwamitin yakin neman zaben APC ya yi karin haske kan abin da ya faru a wajen yawon kamfe a Neja domin Bola Tinubu ya bar wajen kamfe kafin a tashi taro.
Tsohon kakakin majalisar wakilai, Honourable Yakubu Dogara ya bayyana cewa masu tallata tikitin Musulmi da Musulmi a Najeriya suna hauka kuma suna da hatsari.
Saura kiris Atiku Abubakar ya manta da sunan Jam’iyyarsa. Za a ji cewa da aka je kamfe a garin Jos, Atiku ya yi irin subul da bakan da Bola Tinubu ya yi kwanaki
Osita Okechukwu, jigon jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya bayyana cewa Atiku Abubakar ba barazana bane ga takarar Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023.
Gabannin babban zaben 2023, jama’a basu fito ba a gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a jihar Filato. Taron ya kasance a bushe ba mutane.
Bode George ya ce babu hujjar da ke nuna ‘Dan takaran APC, Tinubu daga Legas ya fito, sannan ya nuna idan ba a canza shugaban PDP ba, ba zai zabe ta a 2023 ba.
A cikin daren yau, mai neman mulkin Najeriya a inuwar APGA, Farfesa Peter Umeadi ya kai ziyara zuwa gidan 'dan takaran jam'iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso.
Zaben Shugaban kasan Najeriya
Samu kari