NNPP: Shugaban Jam’iyya Mai Kayan Dadi Ya Yi Murabus, Ya Fadi Wanda Ya Kore Shi

NNPP: Shugaban Jam’iyya Mai Kayan Dadi Ya Yi Murabus, Ya Fadi Wanda Ya Kore Shi

  • Ben Kure ya tabbatarwa jama’a cewa ya bar mukamin da yake kai na Shugaban jam’iyyar NNPP a Kaduna
  • ‘Dan siyasar ya sanar da murabus da kuma ficewarsa daga Jam’iyyar hamayyar mai alamar kayan marmari
  • Kure ya ce ‘Dan takaran Gwamnan Kaduna a 2023, Suleiman Othman Hunkuyi ya sa ya bar jam’iyyar NNPP

Kaduna - Shugaban jam’iyyar hamayya ta NNPP mai alamar kayan dadi na reshen jihar Kaduna, Ben Kure, ya ce ya sauka daga mukamin da yake kai.

Ben Kure ya shaidawa manema labarai cewa yanzu shi ba ‘dan jam’iyyar ba ne domin ya yi murabus. Vanguard ta fitar da wannan rahoto a ranar Alhamis.

Akasin rahotannin da aka yadawa, Kure ya ce ba shugabannin NNPP na Kaduna suka tsige shi ba, shi ne ya aikawa uwar jam’iyyar takardar murabus.

Kara karanta wannan

2023: Babu wani Tinubu ko Atiku, ni zan lashe zaben 2023, Kwankwaso ya hango wani haske

A cewarsa, tun 6 ga watan Disamba 2022, ya sanar da sakatariyar NNPP na kasa ya ajiye aiki, ya ce an yi ta lallabar shi ya yi hakuri ya zauna a jam'iyyar.

Kure ya yi wannan bayani ne a sa’ilin da ya kira taron manema labarai domin ya shaida masu halin da ake ciki da shi a jam’iyya mai alamar kayan dadi.

Rawar da Suleiman Othman Hunkuyi ya taka

Tsohon shugaban jam’iyyar ya zargi Sanata Suleiman Othman Hunkuyi da hana shi tafiyar da jam’iyyar ta yadda mutanen jihar Kaduna za su amfana.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

'Yan NNPP
Wasu magoya bayan NNPP a Najeriya Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Tribune ta ce Kure yana zargin Sanata Suleiman Othman Hunkuyi wanda shi ne ‘dan takarar Gwamnan NNPP a 2023, da neman hana ruwa gudu a jihar.

Na yi abin da zan iya - Kure

“Nayi bakin kokari na, lokaci ya yi da zan yi wani abin da rayuwa ta. Ban ji dadin aiki da jam’iyyar NNPP a jihar Kaduna ba.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Yi Irin Na Tinubu, Ya Tafka Katuwar Katobara Gaban Jama’a Wajen Kamfe

Ba na fatan wani abin ya kara hada ni da mafi yawan shugabannin jam’iyyan Jihar.
Saboda haka ina sanar da ku, magoya baya da abokan siyasa, na sauka daga shugaban jam’iyyar NNPP na reshen Kaduna.
Zan huta, in yi tunanin makomar siyasa ta, sannan in sanar da al’umma a lokacin da ya dace.”

‘Dan siyasar ya ce yana ganin mutuncin Dr Rabiu Musa Kwankwaso har gobe, amma magoya baya ‘dan takarar gwamna suka jawo dole ya bar NNPP.

Ana rigima a Osun

A lokacin da Gwamnan Osun ya ga ya fadi zaben tazarce, an ji labari Ademola Adeleke ya ce sai ya ruga banki ya karbo aron bashin Naira biliyan 18.

A halin yanzu sabon Gwamna Ademola Adeleke yana kukan ya gaji bashin fansho, albashi da biliyoyin kudin da sun fi N400bn daga Gwamnatin Oyetola.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng