Shugaban Kasa a 2023: Majiyoyi Sun Ce Wike Na Goyon Bayan Tinubu Bayan Ya Yi Watsi Da Atiku

Shugaban Kasa a 2023: Majiyoyi Sun Ce Wike Na Goyon Bayan Tinubu Bayan Ya Yi Watsi Da Atiku

  • Majiyoyi sun ce gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yanke shawarar goyon bayan takarar shugabancin Tinubu gabannin babban zaben 2023
  • An yi zargin cewa Wike ya zabi Tinubu ne ganin cewa dan takarar shugaban kasar na APC ya fi takwaransa na Labour Party karfi
  • Gwamnan na Ribas da sauran gwamnonin G5 basa goyon bayan Atiku Abubakar na PDP saboda rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar wanda aka kasa magance shi

Rivers - Rahotanni sun kawo cewa gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yanke shawarar goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, gabannin babban zaben 2023.

Jaridar Punch ta rahoto daga wasu majiyoyi da suka nemi a sakaya sunansu cewa Gwamna Wike ya zabi Tinubu ne bayan ya janye goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

'Muna Bukatar Tinubu Fiye da Yadda Yake Bukatar Mu a 2023', Jigon siyasa

Tinubu, Obi da Wike
Shugaban Kasa a 2023: Majiyoyi Sun Ce Wike Na Goyon Bayan Tinubu Bayan Ya Yi Watsi Da Atiku Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Mr. Peter Obi, Gov Nyesom Ezenwo Wike - CON
Asali: Facebook

A cewar majiyoyin, Wike ya yanke shawarar marawa Tinubu baya, ganin cewa damar da yake da ita a zaben ta fi na dan takarar Labour Party, Peter Obi.

Sun kara da cewa Wike zai ci gaba da zama dan PDP amma zai samawa Tinubu goyon baya a Ribas.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

2023: Akwai yiwuwar Wike zai marawa Tinubu baya, in ji hadimin Ortom

Da yake magana kan ci gaban, wani hadimin Gwamna Samuel Ortom ya ce akwai yiwuwar Wike ya yiwa Tinubu aiki.

Jaridar Punch ta nakalto hadimin na Ortom wanda ba a bayyana sunansa ba yana cewa:

"Gwamna Wike na matukar son shugabancin kasar ya koma kudu a 2023. Idan ka taba halartar wani taro da ya yi mahawara kan wannan, za ka fahimci haka. Zai yi wuya a shawo kansa cewa akwai wani mafita baya ga shugabancin kudu.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa za mu zabi Tinubu a matsayin shugaban kasa – Kiristocin Kudu

"Ya marawa arewa baya a 2019 ta hanyar fitowa fili ya goyawa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal baya. Ya yi tsammanin za a ramawa kudu wannan karamci a wannan karon amma hakan bai faru ba.
"Abin kunya ne ace Ayu, wanda ya kamata ya yi murabus cikin girma don kore tsoron wadannan shugaban yana nan zaune daram-dam. Watakila Wike ya zabi nunawa kowa cewa da gaske yake. Idan Ayu na nan kuma Atiku bai shirya yin wani abu ba, ina ganin Wike zai marawa Tinubu baya. Abu daya na nan a bayyane, ba zai bar PDP ba."

Gwamnonin G5: Wike da rikicin PDP

Gabannin babban zaben 2023, Wike da takwarorinsa na Oyo, Benue, Abia da Enugu wadanda ake yiwa lakabi da gwamnonim G5 sun fito karara sun nuna cewa ba za su goyi bayan Atiku ba idan shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu bai yi murabus dan kudu ya maye gurbinsa.

Yayin da PDP ke ci gaba da cewar ana tattaunawa don sulhu, rikicin ya ki ci ya ki cinyewa a daidai lokacin da zaben 2023 ke kara gabatowa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel