Yan Najeriya Sun Fi Bukatar Tinubu Fiye Da Yadda Shi Yake Bukatarsu, Jigon APC

Yan Najeriya Sun Fi Bukatar Tinubu Fiye Da Yadda Shi Yake Bukatarsu, Jigon APC

  • Babban jigon APC, Alhaji Lanre Onilu, ya magantu a kan babban zaben 2023 wanda ke kara gabatowa
  • Onilu ya ce yan Najeriya sun fi bukatar Asiwaju Bola Tinubu fiye da yadda shi yake bukatarsu a zabe mai zuwa
  • Ya kuma jaddada cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi kokarin da za su yi alfahari da ita har gobe

Kwara - Mataimakin daraktan labarai na kwamitin yakin neman zaben Tinubu./Shettima, Alhaji Lanre Onilu, ya bukaci masu zabe da su kada kuri'u masu yawan gaske ga ubangidansa a zaben 2023.

Onilu ya bayyana cewa yan Najeriya na bukatar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu fiya da yadda shi (Tinubu) yake bukatarsu, jaridar Vanguard ta rahoto.

Jigon na APC ya kuma karyata batun cewa Tinubu na guje ma yakin neman zabe da aikin gwamnati mai ci ta Shugaban kasa Muhammadu Buhari, maimakon haka yake misali da gwamnatinsa a matsayin gwamnan jihar Lagas.

Kara karanta wannan

Jigon APC Ya Bayyana Hanyar Da Tinubu Zai Bi Wajen Samun Kuri’u Miliyan 12 Daga Arewa

Bola Tinubu
Yan Najeriya Sun Fi Bukatar Tinubu Fiye Da Yadda Shi Yake Bukatarsu, Jigon APC Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Ya jaddada cewar lallai gwamnatin APC mai ci ta yi namijin kokari sabanin rade-radin wasu abokan hamayya, rahoton Information Nigeria.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Onilu ya zanta da manema labarai a ranar Laraba, 14 ga watan Disamba a Igbaja, karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara yayin wani shirin bayar da tallafi na hadimin Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq, Kayode Oyin Zubair.

Ya ce:

"Kasar na tsananin bukatar Tinubu fiye da yadda Asiwaju ke bukatar yan Najeriya a yanzu kuma hakan ya nuna a irin goyon bayan da muke samu a dukka jihohin da muka ziyarta."

Kan dalilin da yasa Asiwaju Tinubu ya ki yin kamfen da gwamnatin Buhari, ya ce:

"Asiwaju baya guje masa. Na sha fadin haka sau da dama.
"Buhari ya shafe shekaru bakwai da rabi kuma zan bugi kirji a nan na ce ya yi kokari sosai.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Sun Samu Sabon Sumfurin Shugaba Buhari, Doguwa Ya Jaddada Wanda Ya Dace da Mulki a 2023

"Ku manta duk abun da mutane ke fadi, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kokari kuma muna alfahari da fadin haka kuma za mu gina a kan nasarorin wannan gwamnati.
"Asiwaju zai aikata haka kuma zai yi gyara a duk inda yake akwai kuskure. Buhari dan adam ne dole a samu kuskure.
"Amma a wurin da yake akwai kura-kurai, zai gyara. A ce yana gudun nasara, shin mutane na gudu daga nasara? A'a."

Onilu ya kuma nuna goyon bayansa ga tazarcen Gwamna AbdulRazaq wanda ya ce ya yi kokari sosai a bangaren shugabanci.

Na yi iya abun da zan iya a Najeriya, Buhari

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada cewar gwamnatinsa za ta inganta rayuwar matasa a kasar domin sune ake hange a gaba kan makomar kasar.

Buhari ya kuma bayyana cewar ya yi iya bakin kokarinsa a matsayin shugaban kasa domin Najeriya na da girma kuma matsalolinta na da yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel