Atiku Ya Yi Irin Na Tinubu, Ya Tafka Katuwar Katobara Gaban Jama’a Wajen Kamfe

Atiku Ya Yi Irin Na Tinubu, Ya Tafka Katuwar Katobara Gaban Jama’a Wajen Kamfe

  • ‘Dan takaran Peoples Democratic Party (PDP) a 2023, Atiku Abubakar ya roki mutanen Filato su zabe shi
  • Yayin da yake neman kuri’un jama’a a Jos, Atiku Abubakar ya yi kuskure wajen ambatar sunan Jam’iyyarsa
  • A maimakon a ji ya fadi PDP, sai Wazirin Adamawa ya nemi ya ambaci APC, daga bisani ya yi wuf ya gyara

Jos – Irin abin da ya faru da Asiwaju Bola Tinubu mai neman zama shugaban kasa a jam’iyyar APC, shi ya faru da ‘dan takaran PDP, Atiku Abubakar.

Da aka je taron yakin neman zaben jam’iyyar PDP a garin Jos, jihar Filato, Atiku Abubakar ya yi subutar bakin da ta jawo mutane suke yi masa dariya.

A maimakon Alhaji Atiku Abubakar ya yi kira ga mutanen da suka halarci taron da su zabi jam’iyyarsu ta PDP, sai aka ji yana neman cewa ‘APC’.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na Kasa, Sanata Adamu, Ya Bayyana Magajin Buhari

Kamar yadda bidiyoyin da muka saurara suka nuna, ‘dan takaran shugaban kasar ya fara kiran ‘A...’, a lokacin da yake niyyar cewa a zabi jam’iyyar PDP.

PDP tayi kamfe a Filato

Jam’iyyar adawa ta PDP tayi taron yakin neman zabenta ne a ranar Talata a filin wasa na Rwang Pam a Jos, inda dinbin magoya baya suka halarta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Atiku Abubakar mai neman mulki a 2023 ya yi jawabinsa a Hausa, yana rokon mutanen jihar Filato su mara masa baya ya karbi mulkin Najeriya.

Atiku
'Yan PDP da Atiku Abubakar a Jos Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

“Jama’ar Filato, kamar yadda wannan fili yake da tarihi, kamar yadda ku ka ji, mun zabi MKO Abiola, mun zabi Olusegun Obasanjo.
Shugabannin kasa dabam-dabam muka zaba a wannan wuri. Domin darajar Ubangiji da darajar wannan wuri, ku tabbatar kun zabi A…

Kara karanta wannan

Shugaba a PDP ya Fallasa Tinubu, Kuma Yana barazanar ba Zai Zabi Atiku a 2023 ba

(Ina nufin), PDP a wannan karo. PDP!!!

- Atiku Abubakar

Sai ka ce Bola Tinubu

Hakan ya yi kama da abin da Bola Tinubu ya yi kwanakin baya, ya ce Allah ya yi albarka ga jam’iyyar ‘PDAPC’, an samu rahoto an yi haka ne kuma a Jos.

Kusan wannan ne karon farko da aka ji irin wannan subul-da-baka daga wajen Atiku mai shekara 76, shi kuwa Bola Tinubu ba lokacin ne ya fara tuntube ba.

A wancan lokaci an taso ‘dan takaran shugaban kasar na APC a gaba, amma inda ya sha bam-bam da Atiku Abubakar, shi bai taba sauya-sheka a siyasa ba.

Atiku Abubakar ya yi ta yawo tsakanin APC mai mulki da PDP, don haka wasu suke ganin sunayen jam’iyyun suka nemi su cakude masa wajen yakin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel