Zaben Najeriya
A cewar Zaura, canja kudin da Buhari ya yi ana dab da babban zaben kasar, ya jefa 'yan Najeriya cikin mawuyacin hali wanda ya tilasta su juya wa jam'iyyar baya.
Tsohon shugaban jam'iyyar APC a yankin Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya yi gargadi kan yadda jam'iyyar ke gudanar da mulkinta inda ya ce akwai barazana a 2027.
Hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta INEC ta rantsar da sabbin kwamishinonin zaɓe wadanda zata tura jihohi bayan majalisar tarayya ta amince da naɗinsu.
Jam'iyyun adawa bakwai ne suka hada kansu karkashin kungiyar hadakar jam'iyyu (CCPP) don kawo karshen mulkin APC a Najeriya. Hakadakar za ta bunkasa dimokuradiyya.
Kungiyar CAGRAM ta sha alwashin nemawa Shugaba Tinubu kuri'u a gabanin zaben 2027 da zai ba shi damar yin tazarce. Hakan ya biyo bayan ayyukan Tinubu a Najeriya.
Dr. Muazu Babangida Aliyu ya ce siyasa sai mutanen banza, yake cewa tun daga wajen sayen fam zuwa zaben tsaida gwani, an yi waje da mutanen kirki daga samun mulki.
Dino Melaye, dan takarar gwamna na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben watan Nuwamba ya ce ba zai tafi kotu kallubalantan nasarar jam'iyyar APC ba.
Dan majalisar mazabar Tudun Wada/Doguwa ya zargi jam'iyyar NNPP ta tafka magudi a zaben gwamnan jihar da ya gudana a 2023. Ya ce NNPP ta yi amfani da kuri'un bogi.
Kafin a iya shirya zabuka masu nagarta, Attahiru Jega ya ce akwai gyare-gyaren da ake bukata, daga ciki ayi wa INEC garambawul sannan a gyara dokar zabe ta kasa.
Zaben Najeriya
Samu kari