Wasu Abubuwa Da Suka Taimaka Wajen Rashin Nasarar Kwankwaso

Wasu Abubuwa Da Suka Taimaka Wajen Rashin Nasarar Kwankwaso

Abubuwa da yawa sun faru a lokacin wannan babban zaɓen da ya gabata, waɗanda suka ƙara saita alƙiblar siyasar Najeriya.

Zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023 wanda aka gudanar a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu, zai kawo sauye-sauye da dama a siyasar Najeriya.

Yayin da wasu ƴan takarar suka samu nasara a zaɓen, wasu kuwa nasarar bata samu ba. Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP, yana daga cikin waɗanda Allah bai sanya sun samu nasara ba.

Kwankwaso
Wasu Abubuwa Da Suka Taimaka Wajen Rashin Nasarar Kwankwaso Hoto: Twitter/@kwankwasoRM
Asali: UGC

Mun yi duba kan wasu abubuwa da suka taimaka wajen rashin nasarar, Rabiu Musa Kwankwaso a zaɓen.

1. Rashin samun ƙarbuwa a ƙasa gabaɗaya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Duk da cewa Kwankwaso ya cinye zaɓen shugaban ƙasa a jihar Kano, amma ya kasa lashe zaɓen na ƙasa gabaɗaya.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Manyan Dalilai 4 Da Suka Sanya Atiku Abubakar Yasha Tumurmusa a Hannun Tinubu

Hakan ya faru ne saboda ɗan takarar yana da farin jini ne kawai a Arewacin Najeriya, musamman jihar Kano.

2. Rashin haɗa kai da Peter Obi

Rashin haɗa kai da Kwankwaso yayi da Peter Obi, ya taimaka matuƙa wajen rashin nasarar da ya samu.

Dukkansu dai sun zauna domin samun matsaya kafin zaɓen shugaban ƙasa, amma daga ƙarshe sun yi baram-baram.

3. Jam'iyyar sa ta NNPP bata da ƙarfi

Jam'iyyar NNPP bata da ƙarfi a ƙasar nan domin ba a ko ina aka santa ba. Hakan ya fito fili a sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.

4. Tsarin Ƙarba-ƙarba

Ƴan Najeriya sun nuna basu son ganin wani ɗan Arewacin Najeriya ya cigaba da shugabancin ƙasar nan, bayan shugaba Buhari.

Hakan ya sanya aka yi ta kiran ganin shugabancin ƙasar ya koma yankin Kudancin Najeriya.

5. Wasu abubuwan na daban da suka taimaka wajen rashin nasarar sa

Kwankwaso yayi rashin nasara a zaɓen shugaban ƙasa, saboda ya kasa samun yawan ƙuri'u da kuma kasa samun kaso 25% na ƙuri'u wanda ake son kowane ɗan takara ya samu a jihohin ƙasar nan har da birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Da Zafi Zafi: Jam'iyyun PDP, LP, ADC Sun Buƙaci Shugaban INEC yayi Murabus Tare Da Sake Sabon Zaɓe

Wasu Abubuwa 5 da Suka Taimakawa Bola Tinubu Wajen Samun Nasara a Zaben 2023

A wani labarin na daban kuma, mun tattaro wasu abubuwa da suka taimaka wajen samun nasarar Bola Tinubu, na jam'iyyar APC.

An takarar na jam'iyyar APC ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa na bana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel