Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Cikakken Jerin Jihohin Da Bola Tinubu Na APC Ya Lashe

Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Cikakken Jerin Jihohin Da Bola Tinubu Na APC Ya Lashe

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta kammala tattara sakamakon zaben shugaban kasa na shekarar 2023.

An tattara sakamakon zaben ne a dakin taro na kasa da kasa, ICC, da ke birnin tarayya Abuja karkashin jagorancin shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu.

Bola Tinubu
Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Cikakken Jerin Jihohin Da Bola Tinubu Na APC Ya Lashe. Hoto: Bola Tinubu
Asali: Facebook

Zaben shugaban kasa na 2023: Tattara sakamakon zabe a Abuja

An tattara sakamakon zabe daga jihohi 36 na kasa da birnin tarayya Abuja a mataki na kasa a Abuja. Su ne:

  1. Jihar Ekiti
  2. Jihar Kwara
  3. Jihar Osun
  4. Jihar Ondo
  5. Jihar Ogun
  6. Jihar Oyo
  7. Jihar Yobe
  8. Jihar Enugu
  9. Jihar Lagos
  10. Jihar Gombe
  11. Jihar Jigawa
  12. Jihar Adamawa
  13. Jihar Katsina
  14. Jihar Nasarawa
  15. Jihar Niger
  16. Jihar Benue
  17. FCT, Abuja
  18. Jihar Akwa Ibom
  19. Jihar Edo
  20. Jihar Abia
  21. Jihar Kogi
  22. Jihar Bauchi
  23. Jihar Plateau
  24. Jihar Bayelsa
  25. Jihar Kaduna
  26. Jihar Kebbi
  27. Jihar Zamfara
  28. Jihar Kano
  29. Jihar Sokoto
  30. Jihar Cross River
  31. Jihar Delta
  32. Jihar Ebonyi
  33. Jihar Anambra
  34. Jihar Taraba
  35. Jihar Borno
  36. Jihar Rivers
  37. Jihar Imo

Daga cikin jihohi 36 da Abuja da aka lissafa a sama, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya lashe 12 yayin da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar, shi kuma ya lashe 12.

Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, LP, ya lashe 12 yayin da Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ya lashe jiha daya tak.

Zaben shugaban kasa na 2023: Jihohi nawa Tinubu ya lashe?

  1. Jihar Ekiti
  2. Jihar Ondo
  3. Jihar Kwara
  4. Jihar Ogun
  5. Jihar Oyo
  6. Jihar Jigawa
  7. Jihar Borno
  8. Jihar Rivers
  9. Jihar Kogi
  10. Jihar Zamfara
  11. Jihar Niger
  12. Jihar Benue

Asali: Legit.ng

Online view pixel