Peter Obi Ba Kanwar Lasa Bane, Ya Kamata Tinubu Ya Dama Dashi a Mulkinsa, Inji Tsohon Gwamna Fayose

Peter Obi Ba Kanwar Lasa Bane, Ya Kamata Tinubu Ya Dama Dashi a Mulkinsa, Inji Tsohon Gwamna Fayose

  • Ayo Fayose, tsohon gwamnan jihar Ekiti ya bayyana Peter Obi na Labour Party a matsayin mutum mai magana daya
  • Tsohon gwamnan ya kuma bukaci shugaban kasar Najeriya na gaba da ya tabbatar da ganin cewa ya yi aiki tare da Obi don amfanin al’ummar kasar
  • A cewar Fayose, tsohon gwamnan na jihar Anambra ya zama wani kusa a fagen siyasar Najeriya

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya bayyana cewa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na Labour Party mutum ne wanda ba za a iya razana shi ba.

Da yake zantawa da gidan talbijin na TVC a ranar Talata, 28 ga watan Fabrairu, Fayose ya bayyana cewa zai amfani shugaban kasar Najeriya na gaba inda ya tabbatar da ganin cewa gwamnatinsa ta yi aiki tare da tsohon gwamnan na jihar Anambra.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun yi dabara: Gwamnan APC na Arewa ya taya Tinubu murna, ya yiwa 'yan kasa jawabi

Peter Obi da Gwamna Ayodele Fayose
“Peter Obi Mutum Ne Mai Wayo”: Fayose Ya Sanar Da Zababben Shugaban Kasa Bola Tinubu Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Obi mutum ne mara buri da yawa, Fayose

Da yake bayyana cewa Obi ya zama 'kaya a jikin shugabannin siyasa da dama a kasar, Fayose dan takarar na Labour Party a matsayin mutum mai wayo.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kuma bayyana cewa Obi mutum ne mara buri da yawa kuma yana da zuciyar gaskiya da ake bukata don daura Najeriya kan hanyar ci gaba.

“Ya kamata Peter Obi ya ci gaba da godiya ga Allah idan wannan ba irin damar da aka saba gani bane a Najeriya, Peter Obi ya zama wani lamari a Najeriya.
“Duk wanda ya lashe zaben nan, iddan bai tafi da Peter Obi a mulkinsa ba zai shiga matsala, kuma gwamnatin ba za ta kai inda ake tsammani ba.
“Peter Obi ya zama wani makaranta a yanzu, kun san Peter Obi ya kasance mutum mai wayo, amma haka Peter Obi yake. Za ka Gan shi dauke da jakarsa shi kadai, ya shiga mota shi kadai.

Kara karanta wannan

A Karon Farko, Peter Obi Ya Magantu Bayan Tinubu Ya Ci Zabe, Ya Yi Alkawarin Abu 1 Tak

“Peter Obi mutum ne mai bukatu yan kadan, yana fadin gaskiya, kuma yana da kan-kan da kai. Zai fada maka cewa takalmina don ya sa na wala ne.
“Peter Obi ya cancanci abun da ke faruwa amma bari na fada maka duk wanda ya zama shugaban kasar Najeriya to ya kamata ya tara da mu.”

Kada ka yarda PDP ta shafa maka bakin fenti, Fayose ga Obi

A gefe guda, jaridar Vanguard ta rahoto cewa Fayose ya shawarci Obi da ya guji jam’iyyar PDP don gudun fadawa irin mawuyacin halin da suke ciki a yanzu.

A cewar Fayose, Obi mutum ne mai tsarki kada ya yarda PDP ta shafa masa najasarcewa da PDP ce ta lashe zabe ba za ta ce a soke zabe ba.

A wani labarin kuma, mun kawo cewa Fayose ya taya dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu murnar lashe zabe da ya yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel