Zaɓukan 2023: Jerin Sunayen Gwabnonin 6 Da Suka Rasa Kujerun Sanatoci

Zaɓukan 2023: Jerin Sunayen Gwabnonin 6 Da Suka Rasa Kujerun Sanatoci

  • Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu Baiji Da Daɗi ba, Domin Ya Gaza Zuwa Majalisar Dattawan Da Yaso Yaje
  • Shima Gwabna Ortom Na Jihar Taraba, Ya Sha Kayi, Yayin da APC Ya Bisa Gida Tayi Masa Kwaf Ɗaya
  • Wani Daga Cikin Gwabnonin Yasha Kayi ne A Hannun Mai Taimaka Masa Na Musamman

A wani salo na abu mai ban mamaki, gwamnoni a wannan lokacin sun rasa kujerin sanatocin da suka nema, ba kamar yadda aka saba ba.

Bawai faɗuwar bace abin mamaki, a'a sun sha kayi ne a hannun mutanen da basu kai su komai ba iya mirza wasa salon siyasa ƴar zamani.

Amma kuma duk waɗanda suka samu nasarar, sun kasance masu tasiri ne a yankunan su a siyasance.

Jerin Sunayen Gwabnonin 6 Da Suka Rasa Kujerun Sanatoci.

Kara karanta wannan

Za'a Sake Gina Ƙonanniyar Kasuwar Maiduguri Ta Monday Market Daga Makon Nan - Zulum

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwabna Ifeanyi Ugwuanyi na Jihar Enugu

Ifeany Ugwuanyi
Ifeany Ugwuanyi Hoto: Legit.ng

Farawa da bismillah, Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na ɗaya daga cikin gwamnonin da suka rasa kujerun sanata a zaɓen da aka sanar a 27 ga watan Fabrairu. Ya rasa kujerar sanatan sa ne ga ɗan takarar Labor Party mai suna Okechukwu Eze.

Ugwuanyi dai ya tsayawa jam'iyyar PDP takarar sanata ne domin ya wakilci Enugu ta Arewa ranar zaɓen 25 ga watan Fabrairu, yayin da yake ƙoƙarin kammala mulkinsa na biyu a matsayin gwamna, sai dai yasha kayi hakan bai yiwu ba.

Gwabna Ben Ayade na Cross River

Shima Ben Ayade gwamna ne mai ci a yanzu haka ɗan jam'iyyar APC mai mukin ƙasa, kuma ya rasa fatan da yake dashi na zama sanatan da zai wakilci Cross River North ne biyo bayan zaɓen da aka gudanar a 25 ga watan Fabrairu na 2023.

Kara karanta wannan

Matasa Sun Tare Motar Shinkafa a Zaria, Sun Ɗebe Buhu 29

Gwamnan ya sha kaye ne a hannun Sanata mai ci Jarigbe Agom-Jarigbe wanda ɗan takara ne dake takara da tutar jam'iyyar PDP, ya samu nasara ne da ƙuri'u 76,145.

Ben Ayade Shima Yasha Kashi
Ben Ayade Shima Yasha Kashi
Asali: Twitter

Gwabna Darius Ishaku Na Taraba

Shima yana ɗaya daga cikin gwamnonin da suka sha kayi a zaɓen daya gabata. Darius Ishaku, yayi wa jam'iyyar PDP takara ne kamar yadda aka sani, kuma ɗan takarar jam'iyyar APC David Jimkuta ne yayi masa fintinkau.

Da yake bayyana sakamakon zaben ranar Litinin ɗin data gabata a Wukari, kwamishinan zaɓen Farfesa Solomon Adeyeye yace Jimkuta yayi nasara a zaɓen ne da ƙuri'u 85,415 yayin da gwamnan mai ci yazo na biyu da ƙuri'u guda 45,708.

Darius Ishaku
Darius Ishaku
Asali: Facebook

Gwabna Simon Lalong na Jihar Plateau

Shima gwabnan Plato, Simon Lalong ba'a barshi a baya ba wajen shan kaye. Gwamnan dake kokarin wakiltar Jos South ya rasa kujerar sane a ƙarƙashin jam'iyar APC a hannun Rtd AVM Bali Ninkap Napoleon wanda yayi wa jam'iyyar PDP takara.

Kara karanta wannan

Duniya Rawar Ƴan Mata: Lalong Ya Tunkuyi Ƙasa a Takarar da Yayi Ta Sanata

Da yake sanar da sakamakon zaɓen, kwamishinan zaɓe na yankin, Farfesa Meshak Goyit yace, Bali Napoleon ya samu nasara ne da ƙuri'u 148,844, yayin da gwamnan da baiyi nasara ba ya samu ƙuri'u 91,674 a APC. Sai kuma Labor Party da ɗan takarar sanatan ta samu ƙuri'u 17,325.

Simon Lalong2
Simon Lalong ya fadi shima
Asali: UGC

Gwabna Atiku Bagudu na Kebbi

Shima ba'a barshi a baya ba wajen shan kayi. Gwamna Atiku Bagudu, tuni yasan kayi a ƙoƙarin da yake na zama sanata a hannun ɗan takarar jam'iyyar PDP mai suna Senator Muhammad Adamu Aliero.

Idan za'a iya tunawa, Senator Adamu Aliero tsohon gwabna ne shima. Kuma shine yake wakiltar Kebbi Central, wanda ya rambaɗa gwamnan dake ci a ƙasa.

Bagudu yanzu haka shine shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya na jam'iyyar APC.

Aliero yayi nasara ne da ƙuri'u 126,588, yayin da Bagudu yasha da ƙuri'u 92,389 kamar yadda kwamishinan zaɓe Abbas Bazataya faɗa.

Kara karanta wannan

A Kwantar Da Hankali, Kada a Kaiwa Igbo Hari, Inji Tinubu akan Rashin Nasararsa a Legos

Gwabnan Jihar Benue Samuel Ortom

ortom
Samuel Ortom na Cikin Jerin Sunayen Gwabnonin 6 Da Suka Rasa Kujerun Sanatoci.
Asali: Twitter

Shima Samuel Ortom na Benue ya samu rashin nasara gagaruma yayin daya kasa ɗarewa kujerar sanata da yaso ya ɗare zuwa majalisar dattawa.

Ortom ya samu wannan koma bayan ne a hannun tsohon mai taimakamasa na musamman watau Titus Zam na jam'iyyar APC.

Da yake baiyana sakamakon zaɓen, kwamishinan zaɓen na gundumar, Rufus Shaa’ato, yace Zan ya samu ƙuri'u 143,151 ne yayin da Ortom ya tashi da ƙuri'u 106,882, sai kuma Mark Gbillah na Labor Party daya samu ƙuria 51,950 a matsayin na uku.

Abisa al'ada a Najeriya, gwamnoni na tafiya Sanatoci ne domin wakiltar yankunan su da zarar sun gama wa'adi biyu na mulkin su da kundin tsarin mulkin Najeriya ya basu dama.

To amma ga gwamnonin da suka gaza samun nasara, hakan na nufin kenan, waɗannan gwamnoni bazakaji duriyar su ko tasirin su ba siyasance da zarar angama hada-hadar miƙa mulki.

Kara karanta wannan

INEC Ku Daure, Ku Cije Akan Gaskiya Karku Bari Matsin Lamba Yayi Tasiri Akan Ku - Atiku Abubakar

Mulki kenan, yau gare ka gobe ga wanin ka.

Wasu Abubuwa 5 da Suka Taimakawa Bola Tinubu Wajen Samun Nasara a Zaben 2023

A wani rahoto da Legit.ng ta kawo, ta tattaro dalilai da suka taimakawa nasarar Asiwaju Bola Tinubu na jam’iyyar APC a zaben da aka sanar dashi a matsayin wanda yayi nasara.

Jaridar ta ruwaito cewar Asiwaju Bola Tinubu bai taɓa nuna alamun cire rai da samun mulki ba, babu inda ɗan takaran ya karaya ko ya nuna yiwuwar ya sha kashi a zaɓen na bana.

Asali: Legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel