Sakamakon Zaben 2023: A Karshe Babban Sarkin Yarbawa Ya Magantu Kan Soke Zabe Da Obasanjo Ya Ce A Yi

Sakamakon Zaben 2023: A Karshe Babban Sarkin Yarbawa Ya Magantu Kan Soke Zabe Da Obasanjo Ya Ce A Yi

  • Ooni na Ife ya bukaci matasan Najeriya da kada su yadda ayi amfani da su a matsayin yan tada zaune tsaye don kawo tashin hankali a kasa
  • Sarkin na Yarabawa yayi kiran ne a ranar Talata a wani martani da yayi kan kalaman Obasanjo da ya bukaci a soke zabe
  • Sarkin ya ce duk wani kalaman tuzura zai kara jefa Najeriya cikin wani yanayin na dardar duk da cewa har yanzu akwai wanda ba su farfado daga radadin zanga-zangar #ENDSARS ba

Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwasi, ya yi kira da a zauna lafiya ya kuma roki ma'aikatan zabe su duba hanyoyin da za ayi gyara maimakon soke zaben 2023, Daily Trust ta rahoto.

Arole Oduduwa ya yi kiran ranar Talata, 28 ga watan Fabrairu, awanni bayan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi kira da a soke zabe a wuraren da aka samu tashin hankali lokacin zabe.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Kungiyar ANA Ta Taya Tinubu Murna, Ta Gargadi Obasanjo Kan Yi Wa Dimokradiyya Zagon Kasa

Ooni na Ife
Ooni na Ife ya yi kira ga kasa a zauna lafiya. Hoto: Photo: Ooni Adeyeye Enitan Babatunde Ogunwusi - Ojaja II
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ra'ayin Ooni, ya ce kasar nan bata bukatar kowanne irin katsa landan saboda haka zai kawo barazana ga zaman lafiyar kasar.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya ce:

''Duk fadin duniya, zabe yakan zo da kananan matsaloli. Kuma ana bin matakin doka yadda ya dace don daidaita matsalar kamar ya ke a manyan sassan duniya.''
''Duk yan siyasa da kuma jam'iyyunsu dole ne su yi abin da bazai kawo tarzoma ba saboda haka na iya haddasa wutar rikici ga zaman lafiyar Najeriya.''

Sarkin Yarabawan ya kuma bukaci yan Najeriya da su kwantar da hankali su kuma yi hkr, yana mai bayyana cewa hadin kai da zaman lafiyar kasar gaba suke kowa, duk karfin ikonsa.

Ya ce:

''Najeriya da wasu yan Najeriya har yanzu ba su farfado daga radadin zanga-zangar #ENDSARS ba. Wannan shine dalilin da ya sa dole mu kula da furucinmu.

Kara karanta wannan

“Mu Muka Ci Zaben Shugaban Kasa, Za Mu Kwato Hakkinmu” – Inji Datti Baba-Ahmed

''Yan Najeriya sun sha wahala sosai kuma duk wani tunzuri zai kara radadi kan wanda ake ciki na rayuwar kunci a Najeriya musamman tsakanin talakawa da marasa karfinmu. Ina kuma rokon matasan mu da su jure duk wata tunzura da marasa kishin kasa ke yi don amfani da su a matsayin yan tada zaune tsaye.''

Fayose ya shawarci Bola Tinubu ya dama da Peter Obi a gwamnatinsa

A gefe guda, Ayodele Fayose, tsohon gwamnan jihar Ekiti ya shawarci zababben shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu, ya jawo Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na LP, ya yi aiki da shi.

A hirar da aka yi da shi a TVC ranar Talata, 28 ga watan Fabrairu, Fayose ya bayyana cewa Obi ba mutum ne da za a iya razana shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel