Matsin tattalin arziki
Wani rahoto a kasar Burtaniya ya fitar da jerin kasashen Nahiyar Afirka 10 da suka fi fama da matsalar daukewar wutar lantarki wanda ya ke gurgunta tattalin arziki.
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya kafa wani kwamitin da zai ke ba shi shawari kan tattalin arzikin kasa, musamman duba da yadda kasar ke ci gaba da baya.
An ruwaito yadda dukiyar attajirin da ya fi kowa kudi a Afrika ta ragu bayan da aka samu ragi a darajar Naira a kasuwar duniya a cikin kwanakin nan.
Wani mutum da ya ziyarci shagon siyar da adaidaita ya cika da mamaki bayan an sanar da shi cewa miliyan 2.6 ake siyar da shi a yanzu. Ya daura laifin kan dala.
Jami’an tsaro sun mamaye babbar kasuwar kayayyakin masarufi ta Yankalli da ke a jihar Filato bayan wani yunkurin 'yan daba na satar kayan abinci a ranar Juma'a.
A yau Asabar farashin buhun siminti ya yi tashin gwauron zabi a wasu sassa na jihar Legas, inda ake sayar da shi naira 11,000 amma a Funtua, farashin bai kai haka ba
Mun kawo labarin inda aka kwana game da alkawarin raba kayan abinci saboda ana yunwa. An tanadi metric 42, 000 a cikin 102, 000, za a fara rabawa talakawa.
A game da tashin Dala, wani masani ya haska kuskuren gwamnatin Bola Tinubu. IMF ta ce $1 za ta haura N2000 a 2024, masanin ya taba ba Muhammadu Buhari shawara.
Hukumar kwastam ta ayyana cewa daga ranar 23 ga watan Fabrairu,m za a fara siyar da shinkafa da sauran kayan abinci ga talakawa a Legas da sauran sassa na kasar.
Matsin tattalin arziki
Samu kari