Yunwa: Kungiyar Kwadago Ta Dakatar da Zanga-Zangar Gama Gari, An Fadi Dalili

Yunwa: Kungiyar Kwadago Ta Dakatar da Zanga-Zangar Gama Gari, An Fadi Dalili

  • Kungiyar NLC ta yi bayanin dalilin da yasa ta sanar da dakatar da zanga-zangar kwanaki biyu da ta fara a ranar Talata
  • A cewar shugaban kungiyar kwadagon, an cimma makasudin gudanar da zanga-zangar ne a ranar farko, wanda shine dalilin dakatar da tattakin
  • A ranar Litinin ne gwamnatin tarayya ta gana da shugaban kungiyar kwadagon domin dakile zanga-zangar, amma taron ya tashi baran-baran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Abuja - Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta sanar da dakatar da zanga-zangar da ta shiga na kwanaki biyu a fadin kasar, domin nuna adawa da manufofin tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu.

A karshen taronsu na ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu, kungiyar ta shaida wa manema labarai cewa an cimma manufar gudanar da zanga-zangar ne a ranar farko da fara ta, rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun dakatar da zanga-zangar NLC a Borno a kan wani dalili 1 tak

Kungiyar kwadago ta dakatar da zanga-zangar gama gari da ta fara
Yunwa: Kungiyar Kwadago Ta Dakatar da Zanga-Zangar Gama Gari, An Fadi Dalili Hoto: Nigeria Labour Congress
Asali: Twitter

Sanarwar da shugaban kungiyar ya fitar na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Saboda haka, taron NEC ya yanke shawarar dakatar da zanga-zangar a rana ta biyu bayan da aka samu gagarumar nasara, don haka an cimma mahimman manufofin zanga-zangar na kwanaki 2 a ranar farko."

Kungiyar ta kuma yaba ma daukacin 'yan Najeriya, shugabanni da ma'aikata kan tururwa da suka yi a fadin kasar don yin zanga-zangar lumana kan halin da ake ciki, rahoton Nigerian Tribune.

An shirya zanga-zangar ne sakamakon cire tallafin man fetur wanda ya janyo hauhawar farashin kayan abinci, tabarbarewar tattalin arziki, hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa a kasar.

Zanga-zanga: Gwamnan tarayya ta gana da NLC

Gwamnatin tarayya da Shugaban kasa Bola Tinubu ke jagoranta ta gana da shugabannin kwadago a daren Litinin, 26 ga watan Fabrairu, amma aka tashi baran-baran inda NLC ta ce lallai za ta yi zanga-zangar da ta shirya.

Kara karanta wannan

Hotunan yadda Kanawa suka karade titunan Kano a zanga-zangar kin jinin tsadar rayuwa

Daga nan sai NLC ta tsayar da harkokin tattalin arziki cak a ranar Talata domin yin zanga-zanga.

Shugaban kungiyar kwadagon, Joe Ajaero, ya ce zanga-zangar saboda yunwa da ke kasar ne ba wai don neman a duba karancin albashi ba.

'Yan sanda sun dakatar da zanga-zangar NLC a Borno

A wani labarin, mun ji cewa tawagar rundunar yaki da ta'addanci karkashin jagorancin kwamishinan 'yan sanda ta dakatar da zanga-zangar kungiyar kwadago ta Najeriya NLC a jihar Borno.

Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwar an gudanar da ita ne a fadin kasar a ranar Talata, kuma an fara ta a Borno da karfe 8 na safe amma ‘yan sanda suka dakatar da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel