Sabuwar Dokar CBN Ta Jawo Surutu a Yunkurin Maido Darajar Naira a Kan Dala

Sabuwar Dokar CBN Ta Jawo Surutu a Yunkurin Maido Darajar Naira a Kan Dala

  • Da alama sabon gwamnan babban bankin Najeriya ya shirya zai sa kafar wando daya da ‘yan kasuwar canji da ke rashin gaskiya
  • Yemi Cordoso ya fito da wasu dokoki da ake ganin masu tsauri wajen harkar canji, wasu sun yi maraba da irin hobbasan da ake yi
  • Akwai wadanda suke ganin idan aka muzgunawa ‘yan canji, farashin Dalar Amurka za ta cigaba da hawa a maimakon sauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Kwararru a kan harkar tattalin arziki, ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki sun yi tsokaci a kan sabuwar dokar CBN.

Babban bankin Najeriya ya wajabta ajiye makudan kudi kafin fara sana’ar canji, kuma dole a fadi hanyar samun kudin kasar waje.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun sake kashe bakaken shugabannin ‘yan bindiga da yaransu

Dala da Naira
CBN tana son karya Dala a kan Naira a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Duk wanda zai nemi kudin PTA ko BTA zai karbi 25% a takardu, sai a tura masa 75% ta kafar yanar gizo a sababbin dokokin da aka kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bankin CBN ya fito da tsari mai kyau

Daily Trust ta rahoto cewa Dr. Muda Yusuf wanda shi ne shugaban CPPE ya yi maraba da tsarin, yana ce za a tsabtace kasuwar canji.

A ra’ayin Dr. Muda Yusuf, ‘yan canji suna tafka abubuwa na rashin gaskiya wajen ciniki, saboda haka zai yi kyau a magace barnarsu.

Paul Alaje wanda yana da ido a bangaren tattalin arziki yana tare da Muda Yusuf, amma yana ganin aiwatar da dokokin zai yi wuya.

Wasu sun yabi aikin Gwamnan CBN

Wani Farfesa da ya zanta da jaridar ya yi madalla da gwamnan CBN da ya ce a yi amfani da kafofin zamani a tura abin da ya kai $500.

Kara karanta wannan

Halin kunci: Yan Najeriya sun sako jarumar fim a gaba kan kamfen a zabi Tinubu, ta shiga damuwa

Idan za a san inda ake samun daloli, Farfesan yana ganin za a magance rashin gaskiyar da ake kokarin rage shi da karfi da yaji.

Wasu ‘yan canjin suna ganin muddin ana so Naira ta mike a kasuwar bayan fage, dole CBN ya rika saida kudin waje ga masu canji.

Amma wasu ‘yan canjin sun zargi sabon gwamnan babban bankin na CBN da kawo tsare-tsaren da zai kora mutane daga kasuwanci.

Wasu 'yan canji sun caccaki Cordoso

Yaseer Arafat matashi ne da yake harkar canji, ya fito shafin X yana ta sukar tsarin bankin, yana ikirarin ba su da hannu a tashin Dala.

‘Dan kasuwan ya ce kin saidawa ‘yan canji Dala da CBN ya rika yi ne ya jawo farashin Dala ya tashi, bankuna suka rika samun riba.

Yaseer Arafat yake cewa a lokacin da ake neman kudin guzuri a bankuna, an rika amfani da takardun tafiyan bogi a samu kudin waje.

Kara karanta wannan

Mashawarcin Buhari ya ankarar da Tinubu, an yi mummunan hasashe a kan Naira

Za a gyara dokokin kasa a majalisa

Ana da labari ‘yan majalisa sun fara aiki a kan kundin tsarin mulkin da ake amfani da shi bayan dawowar farar hula domin kawo mafita.

Jihohi za su samu karin iko da kudi, kuma akwai yiwuwar a samar da ‘yan sanda a karkashinsu idan aka gyara kundin tsarin mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel