Yan Daba Sun Yi Yunƙurin Kutsawa Kasuwar Jos Don Satar Kayan Abinci, Jami’an Tsaro Sun Dauki Mataki

Yan Daba Sun Yi Yunƙurin Kutsawa Kasuwar Jos Don Satar Kayan Abinci, Jami’an Tsaro Sun Dauki Mataki

  • Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa wasu 'yan daba sun yi yunkurin kutsawa cikin kasuwar Yankalli da ke Filato don yin sata
  • Rundunar ta ce jami'an tsaron hadin guiwa ne suka samu nasarar dakile yunkurin da misalin karfe 8 na daren ranar Juma'a
  • Shugaban kungiyar 'yan kasuwar Kalli ya ce 'yan dabar suna zargin cewa 'yan kasuwar ne ke kara farashin kayan abinci, "wanda ba haka bane"

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Filato - Jami’an tsaro da suka hada da sojoji, ‘yan sanda da NSCDC sun mamaye babbar kasuwar kayayyakin masarufi ta Yankalli da ke a jihar Filato.

Wannan ya biyo bayan wani yunƙuri da ƴan daba suka yi na kutsa kai cikin kasuwar don satar abinci da sauran muhimman kayayyaki.

Kara karanta wannan

Jami'an hukumar EFCC sun cafke ɗaliban jami'ar Arewa, sun aikata wani babban laifi

Jami'an tsaro sun dakile farmakin 'yan daba a kasuwar Yankallu da ke Filato
Jami'an tsaro sun dakile farmakin 'yan daba a kasuwar Yankallu da ke Filato. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa ‘yan daban da suka hada da maza da mata, sun isa kasuwar ne da misalin karfe 8:00 na daren ranar Juma’a amma jami’an tsaro suka fatattake su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhaji Jamilu Kabiru, shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tun da farko sun kai rahoto ga jami’an tsaron.

Karin farin kayan abinci ba laifin 'yan kasuwa bane - Kabiru

Ya bayyana cewa sun samu labarin cewa ‘yan dabar daga Gangare, Rikkos da sauran wurare za su kai hari kasuwar domin satar kayan abinci.

"Ba mu dauki wannan jita-jitar da wasa ba muka yi gaggawar kai rahoton lamarin ga jami’an tsaro da suka shiga tsakani cikin gaggawa.
"Ba mu ne sanadin hauhawar farashin kayayyaki ba saboda daga kamfanoni muke sayen kayayyakinmu. Ƙaruwar farashin kullum daga kamfanoni ne."

Kara karanta wannan

Jami’an EFCC sun kai samame wurin ‘yan canji a Kano, Abuja da Oyo akan wani dalili 1 tak

Rundunar 'yan sandan ta tabbatar da faruwar lamarin

Bugu da kari, Kabiru ya yi nuni da cewa suna iya kokarin su wajen kayyade farashin kayayyaki a kasuwar domin kowa na fafutukar sayar da kayan da ke hannunsa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce:

“Mun samu labarin tun da wuri kuma tare da hadin kan wasu mutane a kasuwar muka samu nasarar dakile yunkurin."

Farashin buhun siminti ya haura zuwa N11,000 a Legas

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa farashin siminti ya kara tashi a wasu sassa na jihar Legas inda a yanzu ake sayar da buhu akan naira 11,000.

Wannan karin farashin na zuwa ne bayan da gwamnatin tarayya da kamfanonin sarrafa siminti a Najeriya suka cimma yarjejeniya na tsayar da farashin akan naira dubu bakwai.

Wata dillaliyar siminti a Legas, Alhaja, ta bayyana cewa BUA ne ya fara ƙara kudin, sannan sauran suka yi karin farashin da kusan naira 400.

Asali: Legit.ng

Online view pixel