Farashin Siminti Ya Haura Zuwa Naira 11,000 a Legas, ’Yan Kasuwa Sun Yi Karin Haske

Farashin Siminti Ya Haura Zuwa Naira 11,000 a Legas, ’Yan Kasuwa Sun Yi Karin Haske

  • A yau Asabar farashin buhun siminti ya yi tashin gwauron zabi a wasu sassa na jihar Legas, inda ake sayar da shi naira 11,000
  • Wata dillaliyar siminti a yankin Idimu mai suna Alhaja ta ce BUA da Dangote sun ƙara farashin simintin bayan ganawa da gwamnati
  • Sai dai, Legit ta tuntubi wasu 'yan kasuwar siminti a Funtua, jihar Katsina, inda suka shaida cewa ana sayar da buhu akan naira 7,700

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Legas da Funtua - Rahotannin da muke samu yanzu haka na nuni da cewa ana siyar da buhun siminti tsakanin naira 10,000 zuwa naira 11,000 a yankin Idimu dake jihar Legas.

Hakan ya faru ne duk da yarjejeniyar da aka cimma da masana’antun sarrafa simintin da gwamnatin tarayya na cewa a sayar da siminti kan naira dubu bakwai.

Kara karanta wannan

"Ban san me ya hau kaina ba": Matashi ya sheke mahaifiyarsa, ya kona gidansu

Farashin siminti ya haura zuwa naira 11,000 a Legas
Farashin siminti ya haura zuwa naira 11,000 a Legas, ’amma naira 7,700 a Funtua, jihar Katsina.
Asali: Facebook

Wata dillalin siminti mai suna Alhaja, ta shaidawa The Nation cewa ana yaudarar mutane ne kawai da cewa za a sayar da siminti akan naira dubu bakwai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farashin siminti ya karu bayan ganawar su BUA da gwamnati

A cewarta, Dangote ya toshe duk wata hanyar biyan kudi a lokacin da ake tattaunawa da gwamnatin tarayya, kuma kamfanin ya yi karin kudin bayan gama ganawar.

Ta ce:

"An toshe hanyar biyan kudi na kamfanin Dangote a makon da ya gabata, abun mamaki sai muka ga kawai sun yi karin naira dari hudu bayan bude shafin.
"Hatta kamfanin BUA da ke siyar da shi kan naira 3,500, shi ne ya fara karin farashin. Batun wai siminti zai koma naira dubu bakwai karya ne kawai."

Siminti ya fi karfin kananun 'yan kasuwa

Wani dillali da aka tuntuba kuma ba shi da ma kayan a ƙasa. Dillalin da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da gaskiyar maganganun da Alhaja ta fada.

Kara karanta wannan

An debi garabasa: Jama'a sun mamaye 'dan kasuwa bayan da ya samar da shinkafa mai sauki, buhu N58k

Ya ce:

"A wannan lokacin, ban san abin da zan iya yi ba. Siminti ya fi karfinmu a yanzu don ban ma san ta yadda zan sake sayo wani ba.
Farashin naira dubu bakwai da ake yayatawa a labarai ba gaskiya bane. An kara farashin ne da naira 400 bayan da 'yan kasuwar suka gana da gwamnati. "

Buhun siminti a Funtua naira dubu 7,700 zuwa 8,000

Legit Hausa ta tuntubi wasu 'yan kasuwar siminti a garin Funtua da ke jihar Katsina don jin farashin simintin a safiyar yau Asabar.

Abbas Aliyu Tanko ya shaida mana cewa buhun siminti yanzu ana sayar da shi akan naira dubu 7,7000, yayi da a wasu wuraren ake sayar da buhu akan naira dubu 8,000.

Tanko ya ce 'yan kasuwa da dama yanzu sun hakura da kasuwancin simintin saboda karancin jari da kuma tsadar da simintin ya yi.

Wani makwabcin Tanko da ke sayar da siminti a yanzu ya daina ya shaida mana cewa:

Kara karanta wannan

Tinubu yana bakin kokarinsa, ana yunwa a sauran kasashen waje Inji Sanatan APC

"Ni yanzu haka na hakura da kasuwancin simintin, da ma bai wuce in kawo buhu dari zuwa ƙasa ba, to yanzu abun ya fi karfi na gaskiya.
"Tsadar rayuwar ta sa babu kasuwa, za ka kawo ka yi ta ajiyarsa, kullum kuma ana ƙara masa farashi. Yanzu na koma sayar da gawayi."

Bude boda: Gwamnati za ta karya farashin siminti

Tun da fari, gwamnatin tarayya ta gargadi kamfanonin siminti na Najeriya da suka hada da Dangote, BUA da sauran su da su kuka da kansu idan ta bude iyakokin kasar.

Gwamnatin ta ce za ta iya bude iyakokin kasar don shigo da siminti, wanda hakan zai sa ya wadata tare da karya farashin sa a kasuwanni.

A cewar gwamnatin, idan har ta aiwatar da wannan kudirin, to kashin su BUA da Dangote zai bushe saboda babu wanda zai kara sayen simintin su mai tsada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel