Matsin tattalin arziki
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegn Obasanjo ya nemo wa kasar hanyar fita daga matsalar tsadar kaya inda ya ce a nemi shawarar kasar Zimbabwe.
Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi ya amince da biyan ma'aikatan gwamnatin jihar karin albashin naira dubu 30 har na tsawon watanni uku don saukaka masu.
Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa aiki ya yi nisa wajen fara rabon hatsi tan 42,000 kamar yadda Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawari a cikin wannan makon.
Babban bankin Najeriya ya kuduri aniyar dakile hauhawar farashin kayayyaki, kuma zai cire wasu makudan kudi kimanin naira tiriliyan 5 daga bankunan kasar.
Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya fitar da jerin kasashe 10 mafi arziki a Afirka da aka shiga shekarar 2024 tare da fitar da Najeriya daga jerin.
Ministan ayyuka, David Nweze Umahi, ya bayyana cewa yankin Kudu maso Gabas ba shi da dalilin da zai sanya ya shiga zanga-zanga kan tsadar rayuwa.
Sheikh Kabir Gombe ya ba Tinubu shawarar a saye abinci domin a rabawa talakawa. Malamin ya ce idan wahalar rayuwa ta kai bango, abubuwa za su birkice a Najeriya.
Jama’an gari sun sace abinci da aka tarwatsa wurin ajiyan kaya a birnin Abuja. Bisa dukkan alamu jami’an tsaro ba su ankara da wuri ba ko kuwa ba a iya kai dauki ba.
Najeriya ta shiga jerin kasashe ma fi annashuwa da jin dadi a Afrika, kuma ita ce ta 8 a jerin kasashe ma fi rayuwa cikin farin ciki da jin dadi a Afrika.
Matsin tattalin arziki
Samu kari