CBN Zai Cire N5tr Daga Bankunan Access, UBA, GTB, Zenith, Kan Wani Dalili 1 Tak

CBN Zai Cire N5tr Daga Bankunan Access, UBA, GTB, Zenith, Kan Wani Dalili 1 Tak

  • Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sake bayyana aniyarsa na kawar da rarar kudi daga bankin Access, UBA, GTB, Zenith da sauransu
  • Babban bankin na shirin rage samar da kudi a cikin tattalin arzikin kasar don magance matsalar hauhawar farashin kayayyaki
  • Babban bankin na CBN a lokaci zuwa lokaci ya kan janye ko wadatar da tsabar kudi ga bankunan kasar ta hanyar kudin TB da CRR

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Babban Bankin Najeriya ya kuduri aniyar dakile hauhawar farashin kayayyaki, kuma zai cire wasu makudan kudi kimanin naira tiriliyan 5 daga daga bankin Access, UBA, GTB, Zenith da sauransu.

Matakin farko domin cimma wannan kudurin da ya bayyana shi ne karuwar kudin ajiya na CRR da aka samu zuwa kashi 45% a taron tsare-tsaren kuɗi na ƙarshe da aka gudanar.

Kara karanta wannan

Kudin shigo da man fetur ya tashi, farashin lita ya zarce N1, 200 yau a Najeriya

Babban bankin Najeriya zai janye kudin ajiya na bankuna
CBN ba zai cire Naira tiriliyan 5 daga bakuna lokaci daya ba. Hoto: @cenbank (X) Getty Images
Asali: UGC

Kudin ajiya na CRR shi ne kaso na jimillar kudin ajiyar banki wanda ake buƙata don alkinta tsabar kuɗin da banki ke bukatar mallaka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bankunan Najeriya irinsu Access, UBA, GTB, Zenith da sauran su ba za su iya amfani da wadannan kudi da aka ajiye a bankin CBN ba domin zuba jari ko bayar da lamuni.

Babban Bankin CBN zai kwashe rarar kudi

Mohammed Sani Abdullahi, mataimakin gwamnan CBN fannin tsare-tsaren tattalin arziki, ya tabbatar da shirin a wani taro na baya-bayan nan da aka yi da hadin gwiwar 'NGX Group'.

A taron mai taken: 'Neman kasashen waje masu zuba hannun jari', ya yi nuni da cewa tsarin banki yana da gibin naira tiriliyan 5 don cimma kashi 4% na kudin ajiyar CRR.

Kara karanta wannan

NIN/BVN: Akwai yiwuwar bankuna su rufe kudi a akawun miliyan 80 a Najeriya

Sai dai Sani Abdullahi ya ce CBN ba zai cire Naira tiriliyan 5 din daga bankin Access, UBA, GTB, Zenith da makamantansu a lokaci daya ba.

Ya ce CBN zai aiwatar da sabon tsarin CRR ta hanyar da ba za ta kawo cikas ga bankunan ba, inji rahoton Vanguard.

Babban bankin CBN ya sanya wa'adi

A wani labarin kuma, Babban Bankin Najeriya CBN ya bayar da wa'adin kwanaki 30 ga bankunan Najeriya da su rufe asusun ajiyar bankin da ba a hada shi da BVN ba.

A cewar babban bankin, umarnin yana da nufin haɓaka mafi aminci, mafi kwanciyar hankali, da ingantaccen tsarin banki da biyan kuɗi.

Bayanai daga NIBSS sun nuna cewa, a ranar 8 ga watan Afrilu ne aka hada asusun ajiyar abokan hulda miliyan 57.39 da BVN, daga cikin asusun banki sama da miliyan 190.

Asali: Legit.ng

Online view pixel