Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Ya Fadi Hanya 1 da Tinubu Zai Kawo Karshen Tsadar Kaya

Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Ya Fadi Hanya 1 da Tinubu Zai Kawo Karshen Tsadar Kaya

  • Yayin da ake cikin mawuyacin hali a Najeriya, tsohon shugaban kasa, Obasanjo ya nemo wa ‘yan Najeriya mafita kan matsalar
  • Olusegun Obasanjo ya ce tun da Zimbabwe ta taba shiga irin wannan matsalar kuma ta yi nasara, ya kamata a nemi shawarwari
  • Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne a jiya Litinin 4 ga watan Maris yayin wani babban taro inda ya koka kan tsadar kaya a kasar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana yadda Najeriya za ta shawo kan matsalar tsadar kayayyaki.

Obasanjo ya shawarci Shugaba Bola Tinubu kan neman mafita daga kasar Zimbabwe game da hauhawan farashin kayayyaki a kasar.

Kara karanta wannan

Sauƙi ya zo yayin da Gwamnatin Tinubu za ta fara rabon kayan abinci kyauta a jihohin Najeriya

Tsohon shugaban kasa ya nemo hanyar da Najeriya za ta kawo karshen tsadar kaya
Obasanjo ya ce Bola Tinubu ya nemi shawarar Zimbabwe kan tsadar rayuwa. Hoto: Chief Oluseun Obasanjo.
Asali: Getty Images

Wace shawara Olusegun Obasanjo ya ba Tinubu?

Tsohon shugaban kasar ya ce tun da Zimbabwe ta shiga irin matsalar a baya kuma ta yi nasara, za ta iya ba da shawara ga Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olusegun ya bayyana haka ne a jiya Litinin 4 ga watan Maris yayin wani babban taro da ya hadu da bikin ranar haihuwarsa.

Ya ce Najeriya za ta iya koyon wani abu daga Zimbabwe ganin yadda kasar tayi nasarar fita daga matsalar da ta shiga a baya, Tribune ta tattaro.

Mafitar da Obasanjo ya kawowa Najeriya

“Muna cikin wannan matsala ta tsadar kayayyaki amma shin muna da wata kasa da ke da irin wannan matsala a kwanan nan?
“Tabbas akwai kasar Zimbabwe sun fuskanci irin matsalar, bai kamata a ce mun nemi shawarwari game da tsarin da suka bi ba?

Kara karanta wannan

Halin Kunci: Hukumar Kwastam za ta sake rabon kayan abinci karo na 2 bisa sharuda

“Ko da kuwa abin da zamu yi zai iya bambanta, ya kamata mu nemo hanyar fita daga cikin wannan kangi da muke ciki.”

- Olusegun Obasanjo

Wannan na zuwa ne yayin da ‘yan kasar ke cikin wani rin mawuyacin hali na tsadar kayayyaki musamman wanda suka shafi abinci.

Idan ba a manta ba Hukumar Kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar sanarwa cewa tashin farashin kaya a Najeriya ya kai kaso 29.9%, cewar Daily Post.

Tsohon shugaban kasa Obasanjo da tsarin mulki

A baya, mun ruwaito muku cewa, tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana tsarin mulki da ya dace da kasar.

Obasanjo ya ce tuntuni sun batawa ‘yan Najeriya lokaci inda ya ce dole a sauya tsarin da ake bi na gwamnati don ci gaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel