Ramadan: Sanatan Arewa Na Shirin Rabawa Mutanen Jiharsa Tirelolin Abinci 358

Ramadan: Sanatan Arewa Na Shirin Rabawa Mutanen Jiharsa Tirelolin Abinci 358

  • Sanata Abdulaziz Yari Abubakar ya tanadi tireloli 358 na kayan hatsi domin talakawan Zamfara gabannin fara azumin Ramadan
  • An rahoto cewa tsohon gwamnan Zamfaran zai yi rabon kayan a fadin jihar ba tare da la'akari da jam'iyyar mutum ba
  • Sai dai kuma, talakawa musamman marayu da wandanda mazajensu suka mutu ne za su amfana da tallafin kayan abincin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Zamfara - Sanata mai wakiltar Zamfara ta Yamma a majalisar dattawa, Abdulaziz Yari Abubakar, ya kammala shiri tsaf domin share hawayen talakawa a jiharsa.

Kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta rahoto, Yari ya tanadi tireloli 358 cike da kayan hatsi domin rabawa talakawa a lokacin azumin Ramadana.

Sanata Yari zai raba kayan hatsi
Abdul'aziz Yari zai gwangwaje talakawa da abinci a watan Ramadan Hoto: @SenatorAAYari
Asali: Twitter

A cikin wata sanarwa da Hon. Ibrahim Muhammad, shugaban kwmaitin yada labarai na A A Yari ya saki, ya ce kayan da za a raba a sun hada da shinkafa, gero, sikari, da masara.

Kara karanta wannan

Sauƙi ya zo yayin da Gwamnatin Tinubu za ta fara rabon kayan abinci kyauta a jihohin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su wanene za su ci gajiyar kayan abincin?

Muhammad ya ce za a rabawa al'ummar jihar wannan kaya ba tare da la'akari da jam'iyyar da suke yi a siyasa ba domin rage masu radadi a wata mai tsarki.

A cewarsa, tuni kaso 98 cikin dari na kayayyakin suka isa kananan hukumomi daban-daban na jihar domin wadanda za su ci gajiyar kayan tallafin su same su cikin sauki kuma a kankanin lokaci.

Ya kuma jaddada cewar dole wadanda za su amfana da wadannan kayan tallafi su kasance mabukata, musamman marayu, wadanda mazajensu suka mutu.

Daily Nigerian ta kuma rahoto cewa Muhammad ce a za a fara rabon kayan kafin ko ranar fara azumin Ramadan, sannan ya bukaci mutane da su ci gaba da yiwa tsohon gwamnan na Zamfara da kasar addu'a.

Gwamnan Kebbi zai inganta wuta saboda Ramadana

Kara karanta wannan

Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta nemi a kame dan fafutukar raba Najeriya gida biyu

A wani labarin kuma, mun ji cewa Gwamna Nasir Idris na Kebbi ya ce gwamnatinsa ta fara wani yunkuri don tabbatar da ganin ta samar da wutar lantarki na awanni 24 a jihar, a lokacin azumin Ramadana.

Alhaji Idris ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai jim kadan bayan duba ayyukan da ke gudana a Birnin Kebbi, a ranar Litinin, 4 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel