Matsin tattalin arziki
Hukumar da ke tace fina-finai ta kasa (NFVCB) ta haramta nuna duk wani yanayi da ke nuna tsafin kudi, kisa saboda tsafi da shan sigari a fina-finan Nollywood.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa tsauraran matakan da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bijiro da su ne suka ceto tattalin arzikin kasar daga durkushewa.
Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC ta kasa a Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya nuna damuwa kan salon mulkin Bola Tinubu ganin yadda ake tafiyar da gwamnati.
Wani jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Ismaeel Ahmed, ya wanke shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu daga zargi kan halin da kasar nan ta tsinci kanta.
Kungiyar manyan Arewa (ACF) ta dora alhakin wahalhalun da ake fama da su a Najeriya kan wasu manufofi da gwamatin Shugaba Bola Tinubu ta bullo da su.
Babban Bankin Najeriya, CBN ya sake kara kudin ruwa a kasar daga 25.750 zuwa 26.25 bayan dakatar da biyan harajin tsaron yanar gizo da gwamnatin Bola Tinubu ta yi.
A Najeriya, darajar Naira ta sake yin sama inda ta karu da kusan N28 a jiya Litinin 20 ga watan Mayu a kasuwannin gwamnati inda hakan ke nuna karuwarta da 1.89%.
Wani mai sharhi kan harkokin siyasa kuma mamba a kungiyar Dattawan Arewa Farfesa Usman Yusuf, ya caccaki salon mulkin Bola Ahmed Tinubu a Najeriya.
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya a gwamnatin Muhammadu Buhari, Babachir Lawal ya soki salon mulkin Bola Tinubu inda ya ce hawansa ke da wuya komai ya lalace.
Matsin tattalin arziki
Samu kari